Daga karshe Prof Mansur sokoto yayi magana akan Rubutunsa da ja jawo cece kuce
Farfesa mansur Ibrahim sokoto yayi rubuta dazu da ya kawo cece kuce a kafaffen sada zumunta inda wasu ke ganin maganarsa ya soki addini musulunci.
Wasu kuma sun san cewa akwai balaga a magana wanda ba kowane ke saurin fahimta ta ba sai wanda Allah ya kaddara da hakan.
Malam yayi rubuta a shafinsa kamar haka:
“Wayata ta Fadi
Jiya Victor ya tsinci wayata iPhone 12 pro da ta fadi a Zone 2, Abuja.
Victor bai yi wata wata ba da na kira shi ya kwatanta min inda yake na zo na karba.
Wai kuwa da hannun wani “Mamman” ta fada kuna ganin zan same ta?”
Wannan maganar ta jawo mutane sun tsokaci sosai akan wannan maganar inda suke ta fadin albarkacin bakinsa can sai malam ya sake wani rubutu inda yake cewa:
“Fahimta Fuska
Mutane na ta kira na tsakanin masu cewa don Allah in cire post dina na safe da masu cewa don Allah kada in cire. Ban san comments din da ake yi ba don ban duba ba – ina nan cikin meeting akan wata maslaha ta al’umma- amma ba zan rike ma kowa alkalami ko harshe ba tun da ba ni na yi masa shi ba.
Sheikh Yusuf Sambo ya ba mu labarin wata tafiya da suka yi wa’azin kasa wayar wani ta fadi, wata kirista ta tsinta ta kira su suka dawo suka karba a bakin Coci, a karshen labarin kuma wani ya sace ta a filin wa’azi. Wannan shi ne irin abinda ya faru da ni jiya.
Dukkanmu mun san matsalarmu. Amma wannan yana nufin ana zargin dukkan Musulmi? Ko ana wanke dukkan wadanda ba Musulmi ba?
Ban karanta comments dinku ba, kuma ba zan karanta ba. Duk wanda ya zarge ni ko ya zage ni na yafe masa.
Rubutuna kuma ba zan goge ba. Wanda ya fahimce ni daidai ya gode min, wanda ya fahimce ni ba daidai ba ya zage ni kuma na yafe masa.
Wassalam”
Bayan wanan malam ya sake wallafa wani rubutu inda mutane suke da ganin laifin wannan kalma.
“Ko Hausar ce wasu ba su iya ba?
.. in da ta fada hannun wani “Mamman”
daidai yake da “in da ta fada hannun kowane “Mamman”??”