Yan bindiga sun yi ajalin mutane sun kone gidaje,shaguna, rumbu da dukiyoyinsu a kauyen Sakkwato


Wasu yan bindiga da ba’a san adadin su ba sun budewa wuta a wani kauyen gidan buwai da ke karamar hukumar rabah a jihar Sakkwato da ke gabascin Sakkwato sun kai harin cikin daren lahadi misalin karfe 10pm na dare.
Inda sunkayi sanadiyar ajalin mutum hudu tare da raunata wasu mutane inda daya daga cikin waɗanda anka kai asibiti wakilin hausaloaded yana cikin kauyen ake fadin daya daga ciki mace dattijuwa Allah yayi mata cikawa.
Yan bindiga sunyi bi gida gida duk wanda adda dukiya ta dabbobi sunyi awon gaba da su inda har yanzu ba’a san adadin mashu,raguna, tumaki da awakin da sunka tafi da su ba, kuma sun ƙone shaguna sosai sai wanda Allah ya kare, rumbun ajiyar abinci shima sai wanda Allah ya kare duk sun sanya musu wuta.
Wakilin hausaloaded da yake zantawa da daya daga cikin wanda iftila’in ya faru da shi ya bukaci a sakaya sunansa
yana cewa
“Ina jin su sunka dauki buhu sunka cika da kayan shagona sa’an wani ya sanyawa shagona wuta ina ji ina kallo dukiyarta ta ƙone ƙurmumus, bayan dan lokaci na rego koda sun tafi na kashe wutar amma nan sunka kasa sunka tsare har sai da komai ya ƙone ƙurmumus, nan naji wani yace wannan farawa ce zamu ji cigaba”- in mazauni garin da iftila’i ya afka masa.
Sun ƙone mota hudu zuwa biyar shi kuma mashin babur aƙala yakai 20 kamar zantawar mu da mazauna garin ke fadi basu san adadin yawan rumbun ajiyar abinci da mashin din da anka ƙone ba.