Addini

Danganta Malam Ja’afar ga Boko Haram Jahilci ko son zuciya? – sheikh Aliyu Muh’d Sani

Advertisment

Abin da ke janyo wannan shi ne jahilci da son zuciya. Masu danganta Malam Ja’afar ga Boko Haram ‘Yan bidi’a ne da ‘yan Boko Aqida, da kuma jahilai Gulatus Salafiyya. Saboda a wajen duk wani dan bidi’a, Wahabiyawa su ne ‘Yan ta’adda, saboda son zuciya, don Wahabiyawa suna yaki da Bidi’o’insu na shirka da kafirci. Wannan son zuciyar shi ya hadu da jahilcin rashin sanin ka’idojin danganta mutum ga kungiyar ta’addanci. Haka su ma Boko Aqida, suna yakar Wahabiyawa da irin wadannan karerayi ne, don su a kullum abokin fadansu su ne masu Addini.

Alhali ba mai iya hukunci wa mutum da kasancewa dan kungiyar ta’addanci ne sai ya san Akidun Khawarijawa, wadanda suka gina tafiyarsu a kansu, kuma ya san tushen tunanin kungiyar ta’addancin.

Don haka duk wanda ya san Akidar Khawarijanci ya san tun farko ta ginu ne a kan “Tahkimi”, abin da ake kira a wannan zamani da sunan “Hakimiyya”.

Saboda haka duk wanda ya fito yake kafirta Musulmai saboda “Hakimiyya” to shi ne Bakhawarije dan ta’adda. Ma’ana; wanda ya kafirta Musulmai saboda suna bin hukuncin wani wanda ba Allah ba. Hukuncin Dagutai (constitution).

Danganta Malam Ja'afar ga Boko Haram Jahilci ko son zuciya? - sheikh Aliyu Muh'd Sani
Nura Arzai da ya danganta malam Ja’afar da Boko Haram

Wannan ya sa duk wanda ya jefi Wahabiyawa da ta’addanci, don suna bayyana aiyukan shirka da ‘Yan bidi’a suke yi, to shi jahili ne, ko mai son zuciya. Saboda asali a kan “Tahkimi” aka gina Khawarijanci, abin da ake kira “Hakimiyya” a wannan zamani.

Saboda haka, idan ka bibiyi Tarihin gwagwarmayar Muslunci a Nigeria tun 70s, wanda ta faro daga jami’o’i a cikin Kungiyar MSS, tun a wancan lokacin tunanin ta’addanci (kafirta Musulmai saboda “Hakimiyya”) ya shigo Nigeria, ta hanyar littatafan Abul-A’ala al-Maududiy, da littatafan Sayyid Qutub. Littatafan wadannan – musamman Sayyid Qutub – su ne suka fara haifar da tunanin ta’addanci irin na Boko Haram a Nigeria, bayan Zakzaky ya ware daga MSS ya kafa Kungiyar “Muslim Brothers”, wacce ta dauki tunanin Sayyid Qutub, musamman daga littatafansa “Fi Zilalil Qur’an”, da “Ma’alim fi al-Dareeq” (Milestones).

Daga nan Zakzaky ya dauko tunanin cewa; yanzu al’umma tana cikin Jahiliyya, Jahiliyyar Larabawa a lokacin aiko Annabi (saw). Ba don komai ba sai don babu “Hakimiyya” a Nigeria, ma’ana; ana hukunci da Shari’ar Dagutai. Don haka dole a yi “Bara’a”, a yi tawaye wa Gomnati, a rusa ta, a kafa Gomnatin Muslunci, mai Shari’a da hukuncin Allah. Zakzaky ya bayyana wannan “Bara’a” a taron IVC na MSS, a Funtua, a 1980, a jawabinsa wanda aka kira da sunan “Funtua Declaration”. Kuma na hanun daman Zakzaky a wancan lokacin ya tabbatar da cewa; jawabin da Zakzaky ya yi, na “Bara’a” wa Gomnatin Nigeria ya gina shi ne a kan littatafan Sayyid Qutub “Ma’alim fi al-Dareeq (Milestones)”.

Daga nan suka haramta aikin Gomnati, da karatun Boko. Suka yi ta yaga Certificates na karatun da suka yi.

Sa’annan shi kuma Muhammad Yusuf ya bi tafiyar Zakzaky, a nan ya dauko wadannan tunanin, amma daga baya ya rabu da shi, saboda Zakzaky ya koma Shi’a. Kamar yadda wani makusacinsa a wancan lokacin ya tabbatar cewa; tare da Muhammad Yusuf suka yi tafiyar Zakzaky.

To, abin da ‘Yan bidi’a suke cewa; ai Muhammad Yusuf almajirin Malam Ja’afar ne, to in an sallama, to sai a duba karantarwan Malam Ja’afar, shin a ciki akwai kira ga “Hakimiyya”?
Shin akwai kafirta al’umma ta hanyar cewa; ta koma Jahiliyya?
Shin akwai kiran shugabanni da sunan Dagutai, da kiran a yake su, a rusa Gomnatinsu, don a samar da “Hakimiyya” (Gomnati mai Hukuncin Allah)?

Ni dai a sanina ba za a samu kira ga wannar hanya ba a cikin da’awar Malam Ja’afar, amma akwai kira ga wannar hanya a cikin da’awar Zakzaky, wanda shi ne jagoran Muhammad Yusuf kafin su hadu da Malam Ja’afar.

To in wannan ya tabbata, ta yaya mai adalci zai alakanta tushen da’awar Boko Haram ga Malam Ja’afar, ya manta da Zakzaky?

Haba jama’a, ku zama masu adalci mana!
{ولا يجرمنكم شنئان قوم على ألا تعدلوا، اعدلوا هو أقرب للتقوى} [المائدة: ٨]

In kuma ba ka san wannan Tarihin ba ne, me ya sa ba za ka yi shiru ba?
Yanzu ka yarda ka zo kana yada jahilci da son zuciya, saboda kiyayyarka ga Malam Ja’afar?

Wani zai ce ai Malam Ja’afar ya yi wa’azuzzuka masu zafi na sukar Gomnati, har da ambaton daukar makami, to a ilmance ba a kiran wannan kadai da ra’ayin ta’addanci, ra’ayin Khawarijawa, saboda a ciki babu ra’ayin kafirta Musulmai a dalilin “Hakimiyya”. Iyakaci ko da ya kira mutane zuwa ga tawaye wa Gomnati, iya abin da za a masa hukunci da shi -idan Gomnatin Shari’a ce- shi ne irin hukuncin da aka yi wa A’isha (ra), Dalha (ra), Zubair (ra) da Mu’awiya (ra), saboda sun yaki Shugaba Khalifa Aliyu (ra). Wadannan kuwa ba a taba jin wani Mumini ya kira su da sunan Khawarijawa ba. Hasali ma irinsu ne Allah ya kira da sunan Muminai, ya yi umurnin a yi sulhu a tsakaninsu, inda ya ce:
{وإن طائفتان من المؤمنين اقتتلوا فأصلحوا بينهما، فإن بغت إحداهما على الأخرى فقاتلوا التي تبغي حتى تفيء إلى أمر الله} [الحجرات: ٩]

Alhali su kuma Khawarijawa ‘Yan ta’adda, Annabi (saw) umurni kawai ya yi – kai tsaye – da a kashe su.

Don haka a ilimance, babu wanda zai kira wadannan “Bugat” da sunan Khawarijawa ‘Yan ta’adda.

Saboda haka babbar matsalar masu danganta Malam Ja’afar ga ta’addanci ita ce jahilci, musamman idan ya hadu da son zuciya.

Kuma wani abu da kowa ya shaida shi ne; babu wanda ya kai Malam Ja’afar yi musu raddi, har daga karshe ake zargin su suka kashe shi.

Haba Arzai, ina hankalinka yake ne?

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button