Labarai

Barrister Abba Hikima yayi martani akan hukuncin zaben kano

Akwai abubuwan da ni kaina ban gamsu da suba a ɓangaren NNPP – Barr. Abba hikima

Barrister Abba hikima yana daya daga cikin lauyoyin da suke kariya ga mai girma gwamna Engr Abba kabir Yusuf akan shari’ar da ankayi wanda tabbas duk mai bibiyar shafin wannan lauyan ya fadi tabbas ya fadi wanann fargaba.

Abba hikima yayi wannan martani akan wannan sharia a yau asabar domin mutane da dama suna jiran abinda wannan hazikin lauyan ya fadi a shafinsa na sada zumunta.

Barrister Abba Hikima yayi martani akan hukuncin zaben kano
Barrister Abba Hikima yayi martani akan hukuncin zaben kano

“Maganan nan fa daya ce. Idan za’a maka rashin adalci to sai kaga mutum ya zama wani iri. Sai ya ji yaki ji. Ya gani yaki gani. Ga abu a fili amma yaki fahimta. Ko kuma ga adalchi mai sauki amma sai an bi doguwar hanya domin a tabbatar da akasin sa.

Gaskiya ne. Akwai abubuwan da ni kaina ban gamsu da yadda aka tafi da su ba a shariar daga bangaren NNPP. Kuma tun farko na fada. Ana cikin shariar ma kafin azo ga6ar da kusan awa 2 na fadi tsorona.

Amma babu maganar rashin kwarewa a bangaren lauyoyin. Domin SAN 6 ne kuma gogaggu. Har wadanda ba SAN ba daga cikin team din babu wanda bai san shariar zabe ba daidai gwargwado.

Saboda haka da girmamawa ga kotu, bai kamata ace wannan hukuncin aka gabatar ba a fahimta ta.

Ina da yakinin kotunan sama baza su tabbatar da wannan hukuncin ta. Za’a samu sauki.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button