Labarai

Duk Binciken da akayi akan Dcp Abba kyari ba’a sameshi da laifi ba

Duk Binciken da akayi akan Dcp Abba kyari ba'a samesgi da laifi baWannan sako ne mai muhimmanci garemu ‘yan Nigeria domin mu lura da wasu miyagun jaridu wanda wakilan masu aikata miyagun laifuka suka dauki nauyinsu domin su cigaba da yada labarun karya da batanci akan Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari irinsu jaridar Sahara Reporters, People’s Gazette, Punch News da makamantansu
Akwai wani labarin karya wanda wasu jaridu suke yadawa tun satin da ya gabata akan DCP Abba Kyari da hukumar kula da aikin ‘yan sanda na kasa (Police Service Commission) da Maigirma Ministan Shari’ah da kuma rundinar ‘yan sandan Nigeria, suna ta murda bayanin hukumar kula da aikin ‘yan sanda domin su yada sharri da batanci akan Abba Kyari
A cikin sakon takarda da hukumar kula da aikin ‘yan sanda na kasa ta rubuta wa rundinar ‘yan sanda, tace muddin idan ba’a kawo hujja akan DCP Abba Kyari ba to babu wani tuhuma akan DCP Abba Kyari, domin duk tsananin binciken gaskiya da aka gudanar akan DCP Abba Kyari ba’a sameshi da laifin komai ba, don haka hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta bada wa’adin sati biyu a kawo hujja imba haka ba zata wanke DCP Abba Kyari daga dukkan zargi
Duk binciken duniya an gudanar akan DCP Abba Kyari ba’a sameshi da laifi na cin amana ba, kuskure ne guda daga wanda ba wani abu bane, akwai aikin da yayi wanda bai sanar da shugaban ‘yan sanda IGP ba, da kuma bayyana kokarin kare kansa da yayi a shafinsa na facebook ba tare da amincewar IGP ba lokacin da aka fara yada labarin batanci a kansa, wannan shine kawai dan kuskuren da aka samu a tare da shi, amma ba laifi bane
Har ma mutane suna mamaki kan cewa binciken da aka gudanar akan DCP Abba Kyari yayi tsanani da yawa, ko farar hula ba’a masa irin wannan bincike, amma sai gashi sun tsananta bincike akan abokin aikinsu, duk da haka basu sameshi da laifin komai ba
Batun karban cin hanci Naira Miliyan 8 daga Hushpuppi wanda aka danganta da DCP Abba Kyari ana ta yadawa a media ba haka abin yake ba, yadda abin yake shine; wani mutumi ne dan kasuwa ya karbi Kudi Naira Miliyan 8 daga gurin wani mutumi Morgan mazaunin Kasar Dubai ba DCP Abba Kyari ne ya karbi kudin ba, mutumin ya bayyana a gaban kwamitin binciken DCP Abba Kyari cikin mamaki ana kokarin yiwa DCP Abba Kyari sharri, kuma yayi bayanin abinda ya faru, ya gabatar da shaida na transaction details
Mutumin ‘dan kasuwa ne, da kansa ya tura account number dinsa wa Morgan mazaunin Kasar Dubai ya tura masa kudi domin ya saya masa wasu kayayyaki anan Nigeria, Dan kasuwar ya tura account number dinsa a ranar 4-4-2020 Morgan ya tura Naira miliyan 5, sannan a ranar 9-4-2020 ya sake tura masa Naira miliyan 3, ya zama Naira Miliyan 8, sunyi wannan cinikayya a tsakaninsu ba tare da sanin DCP Abba Kyari ba
Mutumin yace bayan kamar sati 6 da tura masa kudi sai aka samu matsala bai sayi kayan ba, ranar 20-5-2020 Morgan wanda yake da zama a Dubai sai ya kawo karan mutumin gurin DCP Abba Kyari ta hannun Hushpuppi, tunda Morgan bai da nambar wayan DCP Abba Kyari, bai taba saninsa ba sai labari, shine sai ya tuntubi Hushpuppi ya turawa DCP Abba Kyari shaidar an tura kudi wa dan kasuwan Naira milyan 5 da kuma miliyan 3 domin Abba Kyari ya gudanar da bincike
Kuma Dan kasuwan ya gabatar da nasa shaidar a gaban kwamitin binciken Abba Kyari cewa tabbas shi ya karbi kudin Naira Miliyan 8 a cikin account dinsa, kuma ya tabbatar wa kwamitin binciken DCP Abba Kyari cewa Morgan ne ya tura masa kudi ba Hushpuppi ba kamar yadda miyagun jaridu suke yadawa
Kuma mutumin ya bayyana cewa yayi mamakin yadda wasu jami’an FBI da wasu jaridu suke kokarin likawa DCP Abba Kyari wannan transaction na kudi, ya musanta cewa ta ya zai kasance Morgan ya tura masa kudi domin ya saya wa Morgan kaya ranar 4-4-2020, sannan a kawo karansa gurin DCP Abba Kyari ranar 20-5-2020 ya kasance an likawa DCP Abba Kyari sharri irin wannan?
Kwamitin da ya binciki DCP Abba Kyari ya binciki wannan mutumi dan kasuwa wanda Morgan ya tura masa kudi Naira Miliyan 8 domin ya saya masa kaya, kuma kwamitin ya gano cewa mutumin tabbas bayanan da ya fada haka yake, kuma ya cire kudin a tsakanin sati guda da aka tura masa a watan 4 na shekarar 2020, sannan ya kashe kudin gaba daya ba tare da ya bawa DCP Abba Kyari kobo ba saboda bai taba sanin Abba Kyari ba sai a lokacin da aka kai karansa
Sannan alkawarin da Hushpuppi yayi a karan kansa a watan 1 na shekarar 2020 cewa zai yiwa wasu mayakan rundinar IRT ihsani wanda suka je har jihohi hudu neman wani mai suna Vincent Kelly wanda ake zargi da aikata manyan laifukan yanar gizo, wanda Kwamitin binciken Abba Kyari suka gano hakan a hiran da Hushpuppi yayi da DCP Abba Kyari ta WhatsApp, an gudanar da tsatsauran bincike ba’a ga inda Hushpuppi ya tura wani abu ba a matsayin ihsani kamar yadda yayi alkawari kuma ya gagara cikawa
Yaran DCP Abba Kyari sun kama Vincent Kelly sun bincikeshi duk a tsakanin sati 4 tare da samun izni daga wata Kotu a Nigeria, wanda Kotu itace ta bada izni wa rundinar IRT ta cigaba da tsare Vincent tare da bincikarsa bisa laifukan yanar gizo guda 20 da ya amince ya aikata tare da abokinsa Hushpuppi da sauran mutanensu ‘yan damfara wanda suke zaune a Kasar Malaysia, Cyprus da South Africa
DCP Abba Kyari ya gabatar wa kwamitin da ya bincikeshi hujja cewa duk bayanan hiransa da Hushpuppi da sukayi a WhatsApp da ake yadawa a kafofin sada zumunta aiki ne na bincike domin ya binciko hallayya da dabi’un Hushpuppi da sauran mutanensa domin ya jawoshi gida Nigeria ya kamashi tunda sakamakon binciken Vincent ya nuna masa cewa shima Hushpuppi mai laifi ne abin zargi da tuhuma wanda ya cancanta a kamashi a bincikeshi, sai dai matsalar ba’a Nigeria yake da zama ba
Kuma bincike ya gano cewa DCP Abba Kyari ya san Hushpuppi na tsawon watanni 9 ne kadai, daga watan September 2019 zuwa watan June 2020 lokacin da aka kamashi a Dubai, babu wata shaida da ta tabbatar DCP Abba Kyari yana da alaka na cin amana tsakaninsa da Hushpuppi, Abba Kyari bai taba neman kobo daga Hushpuppi ba, kuma duk binciken duniya da aka gudanar akan Abba Kyari ya tabbatar da hakan bai da alakar banza da Hushpuppi
Inda ace jami’an FBI sun tuntubi Gwamnatin Nigeria a sirrance da an basu dama sun tattauna da mutumin nan dan kasuwa wanda Morgan ya tura masa kudi Naira Miliyan 8 domin su gano cewa ko mutumin yana da alaka da DCP Abba Kyari jarumin dan sanda wanda ya sadaukar da rayuwarsa, ya yaki masu garkuwa da mutane ya kubutar da dubbanin mutane har da ‘yan kasar Amurka mazauna Nigeria da akayi garkuwa da su a Kaduna, wanda hakan yasa hukumar FBI ta Amurka ta karramashi da lambar yabo a shekarar 2018
Hushpuppi yaso DCP Abba Kyari ya daure abokinsa Vincent bisa laifin fashi da makami don ya shafe shekaru masu yawa a gidan yari, kamar yadda aka gani a hiran da Hushpuppi yayi da Abba Khari a lokacin da Abba Kyari yake kokarin jansa da zance saboda ya masa dabara ya jawoshi gida Nigeria ya kamashi ya bincikeshi ba tare da shi Hushpuppi din ya fahimci haka ba
Don haka cikin wayo da dabara sai DCP Abba Kyari ya bada belin Vincent a matsayin cewa bai da lafiya, alhali ba haka bane dabara ne, inda ace DCP Abba Kyari yana bukatar kudi daga gurin Hushpuppi to da ya likawa Vincent laifin fashi da makami ya kaishi kuto a daureshi shekara da shekaru kamar yadda Hushpuppi ya bukata, to amma baiyi hakan ba, sai Abba Kyari ba bada belin Vincent, wannan ne dalilin da yasa Hushpuppi bai yiwa dakarun IRT ihsani kamar yadda yayi alkawari ba, bayan sunsha wahala sun ziyarci jihohi hudu wajen neman Vincent
Duk wani babban mutum dan kasuwa ko dan siyasa a Nigeria da ya je Kasar Dubai, idan Hushpuppi ya samu labari sai ya nemi ya gana da shi, idan kuma ya samu dama sai ya dauki hoto dashi, akwai hotunan Hushpuppi da manyan ‘yan siyasar Nigeria birjik a kafar yanar gizo
Don haka wannan kira ne ga ‘yan Nigeria akan cewa suyi watsi da labarun karya wanda wasu jaridun da aka dauki nauyinsu suke yadawa akan DCP Abba Kyari, kar ku yadda da wani labari na batanci akan DCP Abba Kyari, ku jira sanarwa a hukumance daga hukumar kula da aikin ‘yan sanda na kasa ko rundinar ‘yan sandan Nigria
Allah Ya albarkaci Nigeria
Wanda ya rubuta:
Barr. JOSEPH B Donald

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button