Labarai

Na daina yin sallah indai basu bani gida naba – wani Dattijo

Wani dattijo da ya fito daga jihar arewacin Nigeriya inda yayi ikirarin cewa bazai sake yin sallah ba inda har ba’a mayar masa da gidansa ba.

Wannan dattijon yayi wani rikici ne da wani akan ya ara masa kuɗi naira dubu goma sha bakwai 17k kacal amma shi mutum yayi ikirarin cewa tabbas sayen wannan gidan yayi.

Mutumin da suke wannan rigima yace wai gida anka sayar masa sai yace to ya kawo dillalai ya kasa , ya kawo shedanu nawa da nashi ya gaza, ya kirawo makwabtana amma ya gaza Shiyasa dalilin haka kanwar shi wannan dattijo ta kai shi wancan kara kotu.

Shi wancan mutumin ya kawo mutane kala kala amma wannan dattijo yayi nasara kotu ta kori karar yace bai yarda ba, kotu tace bari a biyashi bashinsa ayi rubutu yace bai yarda ba, kanen barrister ya rubuta takarda anka biya kuɗin nan kotu dubu goma sha bakwai 17k munka biya amma yace bai amsa, yabar takarda yaki sanya hannu yanzu haka takarda tana hannuna – inji dattjon.

Daga nan shi wannan mutumin ya daukaka kara yakai shi wata kotu nan ne kotun ta karbe gidan suka bashi kuma sunka turani gidan yari,nayi kwana goma sha takwas 18 a can.

Sunyi da’awa cewa wai bana zuwa kotu Shiyasa sunka karbe gidan sunka bashi sunka turani gidan yari.

Bayan dawowata daga kotu bayan yan kwanaki da nayi a gidan yari ina cikin keke napep sunka sanya “handcuffs” anka zo gidana sunka sanya yan sanya sunka tsare ni, sunka shiga gidan ina kallo sunka rushe gidana anka kwashe kayana sunka kawo su cikin ruwa -inji dattijon.

Labarin akwai ban tausai wanda tabbas akwai rashin imani ga bidiyon nan ku kalla kuji bayyani tiryan tiryan.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button