Wata sabuwa! Mahaifiya ta ta amince da tafiya ta zuwa kasar waje domin yin aikin karuwanci – inji matashiya mai shekaru 18
Wata budurwa yar shekara 18 ta shaida cewa mahaifiyar ta ta bata kwarin gwiwa wajen fita kasar waje domin yin aikin karuwanci
Elo Etim yar shekara 18 da rundunar Rapid respond squad dake jihar legas ta kama yayin da take neman fita kasar ta shaida cewa da goyon bayan mahaifiyar ta wajen fitar ta kasar domin yin aikin karuwanci.
An kama ta ne tare da wata Frances Bamidele tare da jagoran su wanda ta jawo kansu ga aikin Martha Edea yayin da suke neman fita zuwa
Abidjan babban birnin tarayyar kasar Ivory coast .
Da take bada amsar tambayoyi Etim tace:
“Na san cewa Madam Martha zata tafi damu kasar waje domin yin aikin karuwanci kuma mahaifiya ta tana sane da haka itama
Ta bani kudi ma kuma tana mai cewa da in ba yara kanana dake unguwa gwara in tafi inyi kudi da jikina tare da tura mata kudin kashewa.
Tayi min addu’ar samun nasara a sana’ar kuma ta yarda nayi aikin”.
Jagoran tafiya kuma gawurtacen mai safara da mutune zuwa kasashen waje domin aikin karuwanci Martha Edea ta sanar cewa itama ta dade tana harkar karuwanci a Abidjan kuma bayan ta biya bashi dake kanta ta samu yancin daga uwargidan ta wanda ta kaita kasar.
Bayan ta samu yanci ne ta fara safarar mata zuwa kasar domin itama ta samu kudi.
Yayin da jami’an RRS ke bincike a cikin jakar ta sun gano wasu kayan shafe-shafe biyu wanda ta shaida masu cewa tsibbu ne wanda ke taimakawa wajen samun farin jini daga mazaje da kuma kariya daga miyagun yanayi.
Jami’an dai sun mika su ga hukumar dake lura da masu safarar mutane zuwa kasashen waje ta
NAPTIP.