Labarai

Bidiyo: yadda Matasa sunyiwa Kashim shettima ihu yunwa yunwa a kano

A yanzun nan majiyarmu ta samu wani mummunan labari wanda wani fitaccen marubuci nai mai Amfani da kafar sada zumunta ta Facebook Comr Abba Sani Pantami ya wallafa yadda mata suke kiran mai girma mataimakin shugaban kasa kashim shettima ihu na kira da gayamasa cewa akwai yanzu kamar yadda marubucin ya ruwaito.

Tun a shekaran jiya da dare, nace muku na samu labarin cewa an yiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ih*un yunwa-yunwa a jihar Kano.

Idan baku manta ba a ranar jumma’a da ta gabata mataimakin shugaban kasar Najeriya, yaje jihar Kano wurin daurin Auran dan Sanata Barau da ‘yar gidan Aliyu Madaki, ance Kashim yana dagawa mutane hannu domin gaisuwa, Mutane suna bude baki da karfi suna cewa yunwa-yunwa Kashim, kamar yadda za kuji a cikin bidiyon.

 

A yadda na fahimci ihun nasu bana zagi ko cin mutunci bane, sun yi hakan ne domin su isar mishi da sakon halin da al-umma suke ciki ne.

Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kare gane cewa al-ummar Najeriya suna cikin mayuwancin halin da basu taba shiga irin shi ba. Allah ya kyauta.

Mun tattaro kadan daga cikin martanin mutane inda sunkayi tsokaci a karkashin Wannan bidiyo.

@Likitan Dabbobi cewa yake :

Daga nan ya kamata su ankara su san Halin da ake ciki

Allah ya kyauta.

@Dalhat habib sani cewa yake:

Hmmm babu abinda zai canza an gaya muku basu san halin da talaka yake ciki bane wlh sun San komai mudai Allah yakawo mana sauki Ameen .

@ahmed m fulani 2023 yace yake :

Tabbass Wannan Maganar Taka Haka Take #MalamComred.

 

Yakamata Kam Gomnatin Tarayya Tasan Halin Da Ake Ciki ….Allah Ya Kyauta Ya Kuma Dubi Halin da Ake Ciki …..

@muhammad inuwa Auwal cewa yake : 

Comr. Irin wadannan post din kayi hankali dasu, saboda kasan waye kashin shateema, Allah ya sawake.

@Ahmed Abdulqadeer cewa yake :

Allah ya kyauta Wlh ba laifin su bane tsadar Rayuwan ne tayi yawa…pls Consider us Sir munsan komai daga Allah ne Amma kuna da mafita a matsayin ku na Shu’agabanni.

@umar Abubakar mubi cewa yake :

Kokarin yan Arewa kenan Abinci indai za’a basu ko duk za’a karesu basa gani shiyasa har Abada idan bamu gyara ba bazamu iya zaɓarwa Kanmu mafita ba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button