Mutane sunyiwa Abba elmustapha wankin babban bargo da ya wallafa hotunan Sabon Shataletale da Tsoho
Sabon shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Abba Elmustapha, yasha cacca a shafinsa na Twitter a lokacin da yayi tambaya akan sabon Shataletalen dake kofar gidan gwamnatin jihar.
Shugaban hukumar tafe finafinai abba elmustapha ya wallafa hotunan a shafinsa inda yake tambaya:-
“DON ALLAH MUYI ALKALANCI
A cikin Wadannan SHATALETALEN Wanne ne yafi ma’ana, tsari da amfani???”
DON ALLAH MUYI ALKALANCI
A cikin Wadannan SHATALETALEN Wanne ne yafi ma’ana, tsari da amfani???#abbanaabba2027 pic.twitter.com/R0bcYgScm9
— Abba El-mustapha (@abbaelmustaph1) August 19, 2023
Wadannan sune kaɗan daga martanin da mutane sukayi masa munka tattaro muku.
@bukar huasaini cewa yake: Kai kasane adalci kuwa ya xakayi wanna magana Ana ciwar ayi adalci Kai kanka kasane cewa akwai aikin dawano a wajin
Kamar Dai Haka.
@farouq_us shi kuma yana cewa : @all Yan kwankwasiyya basu da technology wlhi
@Gentle_kabir yana cewa : My friend Kawai Ka More Kugerarka Ka Kyale Mu. Ko Makaho Yasan Abu me Kyau inyashafa. Anamaganan Al’ada, kyau, nagarta da inganci kaikuma Magana na siyasa da molonka. Kudai Bakuso ace daga kunfito Govt house, Aikin Ganduje Zaku Fara Gani. Shiyasa KUKA Rushe Tsohon! Shine Kawai…
@abdulwaheedsal19 yana fada cewa: Tin ynxu ka fara Gane bbu gsky a tafiyar taku bbu Wanda ya goyi bayan Wanda aka sakeyi kaima kasan gsky kwai baxa ka fada ba SBd knada mukami a ciki ……adaiyi mgn in tusa tana hura wuta
@kabirshuaib3 yana mai cewa: Ana maganar ma’ana kuna maganar kyau,
Wanda akayi sabo shine yafi maana da tsari,
Kana ganin ko INA,
Kalli yadda tsarin gidan kwamnati ya fito, da sauran gurare,
Kana ganin Wanda ya fito ta kowanne bari
In al’ada kuke nema Ku tafi masarauta .
Sabon yayi kyau yayi maana
@hauwaeu cewa take: Wannan yafi kyau. Gashi ana ganin koina da koina. Wuri yayi haske.
@abubakarkabirT2 yana mai cewa : Alh Bulama wannan kawai saboda Sabuwar Gomnati tazo ne kuke cewa haka, Amma ada lokacin da akayi waccen din kowa ya yaba da ita.
Saboda haka idan wata Sabuwar Gomnatin ta sake zuwa zata sake rushewa itama tayi Wanda take ganin yafi Mata kyau.
Zamani kowa da nasa ai.
@hamzasuleiman cewa yake : Ba an maka SA ba dole tace ayi alkalanci. Ina zaka hada wanan abun da na baba janduje . Allah yasa mu dace.
@it’s_bbsh yana cewa : Na ganduje yafi kyau kuma ya fito da al adun arewa
Ko turawa sakazo kano zasu gane sunzo africa kuma arewa.
@bello rabiu isa cewa yake : Ko makaho yasan na ganduje yafi kyau da tsari. Kuma zancen da ake cewa wai yana kare ganin mai tuki karyar banza ce daman mai dukin bai san dokokin tuki bane shi yasa.
Mutane sai tofa albarkin bashin su suke anan Wannan al’amarin.