Labarai

Talakawa Ba Za Su Shiga Aljanna Ba – Inji Wani Minista

Wasu kalamai da wani babban dan siyasa yayi sun jawo magan ganu saboda tsaurin maganar kamar yadda mutane suka tabbatar

Labarin da muke samu daga jaridar Aminiya ya shaida mana cewa Ministan Cikin Gida na Uganda, Mista Kahinda Otafire ya shiga cikin tsaka-mai-wuya sakamakon wasu kalaman da ya yi da ke nuna cewa talakawa ba za su shiga Aljanna ba.Talakawa Ba Za Su Shiga Aljanna Ba – Inji Wani Minista

A cewar Ministan dai, talakawan ba za su Aljannar ba ne saboda sukar da suke yi wa Ubangiji wajen gabatar da korafe-korafe kowace rana.

Ministan yayin jawabi ga wani taron dalibai a Kyenjojo, ya shaida musu cewa kada su zargi Ubangiji idan sun kasa amfani da damar da Ya ba su na yakar talauci, inda ya umarce su da su
jajirce wajen samun arziki maimakon korafin da suke yi kowace rana.

Mista Otafire ya ce kuskure ne mutane su rika gabatar da korafe-korafe
da kuma zargin Ubangiji ba tare da tashi tsaye wajen yin ayyukan da za su samar musu da kudade ba.

Ministan ya ce wannan hali na sukar Ubangiji da talakawa ke yi zai hana su shiga Aljanna.

Wadannan kalamai sun haifar da ce-ce-ku-ce a kasar inda wadansu malaman addinai da kungiyoyi suke zargin gwamnati da gazawa wajen samar da yanayi mai kyau da talakawa za su samu sauki daga halin kuncin da suka samu kansu.

Kasar Uganda na daya daga cikin kasashen da ke da dimbin matasan da ba su da ayyukan yi. (Rfi)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button