Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Bello Yabo yayi alla-wadai da gidajen rediyon Vision da Garkuwa FM dake Sokoto kan yadda suka himmatu a cikin labarunsu wajen saka muryar Bello Turji a lokacinda yake ƙoƙarin karyata shi a wata hira da jaridar Aminiya tayi da shi kamar yadda shafin sokoto facts ya ruwaito a shafin na facebook.
Bello Yabo yace akwai ban mamaki kwarai da gaske ace cikin tambayoyi kusan 50 da aka yiwa Dan ta’adda Turji gidajen rediyon su kasa bada labarin ko daya face wadda ake ƙoƙarin karyata abinda ya bada bayani kamar yadda aka sanarda shi.
“In Vision FM tayi, ita ban mamaki amma dai ace, sukar Bello Yabo, kiyayya da Bello Yabo Garkuwa FM, wallahi nayi mamaki! wallahi Allah Ya sani nayi mamaki!! Don ban aza makiya na bane amma tunda haka ne, Bisimillah, a cigaba”
“Bello Yabo ba makaryaci bane, ku fadawa Garkuwa FM Bello Yabo ba makaryaci bane, ku fadawa Vision FM Bello Yabo ba makaryaci bane” – inji Sheikh Bello Yabo.
https://youtu.be/t1czIXYuALs
Ban Taɓa Sanin Cewa Yin Garkuwa Da Mutane Laifi Ne A Dokar Kasa Ba, Cewar Jamilu Sa’idu
Matashi Jamilu Sa’idu Dan Shekara 28 Da Haihuwa Dake Garin Jiƙamshi A Karamar Hukumar Musawa Ta Jihar Katsina Da Ake Zargi Da Razanar Da Mutane Akan Zai Yi Garkuwa Da Su.
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina Ta Yi Nasarar Kama Shi Bayan Da Ya Kira Wani Abdulsalam Hassan Dake Kauyen Sabon Garin Dan Bajida Dake Karamar Hukumar Bindawa Akan Cewa Ya Ba Shi Naira Dubu Ɗari Biyu Ko Ya Yi Garkuwa Da Shi.
Amma Wanda Ake Zargin Ya Bayyana Cewa Shi Bai San Cewa Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutane Laifi Ba Ne.
Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa Ya Ce Da Zaran An Kammala Bincike Za’a Gurfanar Da Shi Gaban Shari’a.