Labarai

An yanke wa Sarkin ‘yan kirifto hukuncin shekaru 25 a gidan yari

Wata kotu ta yanke wa Sam Bankman-Fried Sarkin ‘yan crypto zaman gidan yari na shekaru 25.

Bankman-Fried fitaccen ɗan kasuwa ne da babu irinsu da yawa – ya yi shahara mai ƙarfi a kafafen sada sumunta, abin da ya sa ƙanana da matsagaitan masu hada-hadar crypto ke bin shafinsa.

Manyan masu zuba jari sun amince da shi, saboda yadda kasuwanci ke haskakawa kuma ya samu karbuwa a duniya, dalilin da ya sanya suka sanya miliyoyin suƙinsu kenan a kamfaninsa.

Yana yawan nuna kansa a matsayin kwararre kuma ɗan baiwa a lissafi wanda bai damu da tara duniya ba.

Biloniyan ya taɓa tuka wata motar iyalai da ta rakwakkwaɓe kuma ya sha kwana kan buhun waje a ofishinsa. Yana da burin taimakawa ƙungiyoyin baimakawa al’umma.

Kamfaninsa na musayar kuɗi na crypto ya bunƙasa ya sama na biyu mafi girma a duniya inda suke hada-hadar dalar Amurka biliyan 10 zuwa 15 a rana.

Kamfanin Samuel Hapak ya wakilci masu zuba jari 200 a zaan kotun waɗanda suka yi asarar kuɗi da suka kai dala miliyan 35 lokacin da kamfanin FTX ya bayyana yana daf da durkushewa.

Shugaban kamfanin samar da manhajar kwamfuyuta na Wincent ya shaida wa BBC cewa ɗaurin da aka yi wa Sam na shekara 25 ya yi daidai.

Kamfanin Wincent ya yi asarar rabin jarinsa kimanin dala miliyan 70 – kashi 25 na hannun jarinsa, Hapak ya shaida wa BBC.

-BBC hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button