Labarai

Bodi: Kabilar da mata ke rububun maza masu rusa-rusan ciki

Kabilar Bodi ko Me’en su na rububin maza masu katon tumbi. Su na zaune ne a yankin tafkin Omo da ke Ethopia kuma babban abin burgewa dangane da kabilar shi ne yadda mazansu ke shan jini da madarar shanunsu don suyi kiba, Nigerian Pulse da LH na ruwaito.

Kabilar da mata ke rububun maza masu rusa-rusan ciki
Kabilar da mata ke rububun maza masu rusa-rusan ciki

Yayin da ake saura watanni shida ayi gasar neman aure, iyayen za su zabi namiji guda wanda zasu shirya don shiga gasar. Yana tafiya ne wata bukka inda zan dinga shan jini da kuma madarar shanu, sannan ba zai kusanci ko wacce mace ba yayin shirin.

Da garjin rana zai yi sauri yasha jinin yadda zai shiga jikinsa da kyau, amma sakamakon kyankyani, akwai mazan da su ke yin amai. Bayan watanni shida da fara shan jinin, mazan za su fito don kowa ya nuna katon cikinsa kuma daga nan za a dauke su a jarumai har karshen rayuwar su.

A ranar gasar, mazajen za su nuna cikinsu wanda za su shafe shi da toka da kasa. Akwai mazan da tsabar kibar da su ke yi ko tafiya ba sa iyawa dakyau. Bayan sun shafe jikinsu da kasa da toka su na fitowa ne daga bukkokinsu inda za a fara gasar.

Su na zagaye wata bishiya ne yayi da mata ke basu giya su na kambama su su kuma su na sharbar zufa. Duk namijin da yafi sauri yayin zagayen ne za a zaba sannan za a yanke sa.

Bayan kammala shagalin zai dage wurin sabe kibar da yayi don ci gaba da rayuwarsa ta yau da kullum. Sai dai ko wanne namijin yana da burin kasancewar namijin da yafi kowa kiba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button