Gawurataccen Lauyan Najeriya zai tsayawa wanda ya zagi Annabi S.a.w A kotu
Ana kokarin daukaka karar Yahaya Aminu Shariff zuwa gaban babban kotu
– Kotu ta samu Yahaya Aminu Shariff da laifin cin mutuncin musulunci a baya
– Wannan ya sa Alkalin karamin kotun shari’a ya yanke masa hukuncin kisa
Ana kishin-kishin din cewa shahararren lauyan nan, Femi Fakana SAN, zai tsayawa Yahaya Aminu Shariff wanda aka yankewa hukucin kisan-kai.
Babban Lauyan zai kare wannan matashi mai shekaru 22 da haihuwa da Alkali ya samu da laifin cin mutuncin addinin musulunci a jihar Kano kwanakin baya.
Rahotannin da su ke zuwa mana a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, 2020, sun bayyana cewa Femi Falana ya samu karbar takardun wannan shari’a da ake yi.
Hakan na zuwa ne makonni uku da samun Aminu Shariff da laifi a gaban wani kotun shari’a. Falana zai tsaya wajen ganin an daukaka kara domin a saki matashin.
Mai magana da yawun bakin bangaren shari’a na jihar Kano, Babajido Ibrahim, ya sanar da manema labarai wannan cigaba da aka samu a shari’ar dazu da rana.
Mista Babajido Ibrahim ya ce takardun wannan kara da zaman kotun da aka yi sun kai ga Femi Falana, a madadin wani Lauya da ya aiko ya wakilce sa a jihar Kano.
An gabatarwa wakilin Femi Falana SAN wadannan takardu ne a ranar 2 ga watan Satumba. Wannan zai bada damar lauyan ya kare wanda ake tuhuma a gaban kuliya.
Legit ta kara da cewa Falana wanda ya yi fice wajen kare hakkin Bil Adama, zai duba hukuncin da Alkalin kotu ya yanke a watan Agusta, daga nan ya garzaya kotu, ya daukaka wannan shari’a.
Wannan shari’a ta jawo ce-ce-ku-ce har a ketare, inda wasu su ke ganin bai kamata a yankewa mutum hukuncin kisa a kasar da kowa ya ke da ‘yancin yin magana ba.
A gefe guda, masana addinin musulunci sun yaba da hukuncin da Khadi Aliyu Muhammad na kotun shari’a da ke Hausawa ya yi, sun ce haka addinin musulunci ya tanada.