Buhari Na Shan Kunya A Idon Al’ummar Nijeriya, Inji Sanata Shekarau
Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel
Tsohon gwamnar jihar Kano, kuma Sanata mai ci a halin yanzu Malam Ibrahim Shekarau, ya ce “naka shike fara ba da kai, kafin na waje su yi maka yeho”.
Sanata Shekarau a inda ya ci gaba da cewa a duk iya irin kamanta adalcin ka sai wani ya ga gazawar ka, daman irin wannan rana yake jira. Ba kuma za ka ji yana shelanta alherin ka ba, har sai idan ya ji ka yi ba daidai ba, domin ya samu hujjar muzanta ka a fuskar al’umma.
Bayan haka, Shekarau ya ci gaba da cewa Shugaba Muhammad Buhari, mutum ne mai tsaurin gaske, musamman akan gudanar da harkokin mulki amma a bisa adalci da tausayawa, da kiyaye amana, koda ko na kusa da shi zai ci amanar da zaran Shugaba Buhari ya sani, nan take za a dauki hukuncin da ya dace da shi.
Shekaru ya kara da cewa na kusa da Shugaba Buhari ne wadanda suke fara ba shi kunya domin kuwa ganin yadda ya aminta da su ya kawo su domin su yi aiki domin Allah da kuma riko da amana, amma duk da haka gwamnati ba zata tauye masu ha’kkin su ba na albashin su, amma duba ga yanda suka san Buhari, a matsayin mutum mai kiyaye Amana, amma duk da haka saida suka ci amanar sa, suka kuma ci amanar al’ummar Nijeriya.
Dun haka dole ne Shugaba Buhari ya ‘kara taka tsam-tsam kan sanin wadansu mutane ne zai dam’ka masu amanar Al’umma, da sanin waye shi tun kafin a aminta dashi, don gujema Shiga kunyar al’umma.
Tsohon gwamnan ya yi wannan bayanin ne a inda yake bada shawara a zauran Majalisar sanatoci dake Abuja, domin ciyar da kasa gaba.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





