Duk Kanwar Jace : Buhari da Trump Ba Su Damu Da al’ummar Su Ba – Wizkid
A karon farko, fittacen mawaki Wizkid, ya yi magana a kan salon jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka, Donald Trump
– Wizkid ya tofa albarkacin bakin sa kan kisan mutane da jami’an ‘yan sanda ke yi a kasashen biyu ba tare da hakki ba
– Mawakin ya yi Allah wadai da halin ko in kula da shugabannin biyu su ke yi kan yadda jami’an ‘yan sanda suka mayar da ran farar hula ba a bakin komai ba a kasashen biyu
Ayo Balogun, shahararren mawaƙin Najeriya wanda aka fi sani da Wizkid, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da takwaran sa na Amurka, Donald Trump, ko kadan ba su da damu da al’ummar su ba.
Cikin wani sako da ya wallafa a kan shafin sa na Twitter, gogarman mawakin ya ce banbancin da ke tsakanin shugabanin biyu shi ne kwazon Trump na iya amfani da dandalin sadarwa na Twitter.
Wizkid ya ce Buhari ya jahilci iya amfani da dandalin na sadarwa, lamarin da ya ce shi ne kadai banbancin da ke tsakanin shugabannin biyu.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Wizkid wanda bai taɓa yin sharhi ko furuci a kan kowane dan siyasa ba, a yau ya ba ‘yan Najeriya mamaki da sauran al’ummar duniya.
Mawakin ya yi furuci a kan shugabannin biyu, biyo bayan yadda jami’an tsaro na ‘yan sanda ke kashe mutane ba tare da wani dalili ba a kasar Amurka da kuma nan gida Najeriya.
A kwanakin nan ne dai tarzoma ta barke a biranen Amurka, biyo bayan kashe wani bakar fata, George Floyd, da wani jami’in ‘dan sanda na reshen garin Minneapolis ya yi
Zanga-zanga dai kan wannan zalunci na ‘yan sanda na cigaba da yin karfi a biranen Amurka kamar yadda kafofin sadarwa suka tabbatar.
Mutuwar Ba’Amurken ta zo ne tun gabanin kurar mutuwar wata budurwa mai suna Tina Ezekwe ‘yar shekara 16, da wani jami’in ‘dan sandan Najeriya ya kashe a jihar Legas.
Wannan lamura biyu sun haddasa fushi a Najeriya da kuma duniya bakin daya, inda mutane da dama ke amfani da shafukansu a zauren sada zumunta wajen nuna rashin jin dadi tare da neman adalci.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, Wizkid ya yi Allah wadai kan yadda jami’an ‘yan sanda ke yi wa farar hula kisan mummuke ba tare da wani haddi ba.
Kamar yadda wallafa a ranar Asabar: “‘Yan sanda na kashe bakaken fata a Amurka, kuma ‘yan sandan Najeriya na kashe ‘yan kasar su. Ba bu wanda zai jibinci wannan lamari sai dai gyaran Allah.”
Police dey kill black Americans and Naija police dey kill Nigerians. No man fit sort this matter. God save us— Wizkid (@wizkidayo) May 30, 2020
Buhari/Trump same person lol only difference be say one sabi use twitter pass the other. Clueless!— Wizkid (@wizkidayo) June 1, 2020
God save the world ! Save the people ❤— Wizkid (@wizkidayo) June 1, 2020
Sanarwa da ta biyo baya a ranar Litinin, fitaccen mawakin ya ce gazawar shugabannin biyu wajen daukar mataki a kan kisan da jami’an tsaro ke yi, “ya nuna cewa al’ummarsu ba ta dame su ba.”