Miji ya kashe matar shi saboda ta bincika mishi waya
Matar tayi bincike a wayar mijin
Matar mai suna Mirriam Joni, yar shekara 27 dai bata wuce wata 3 da auran mijin nata ba. Majiyar mu tace ta ɗauki wayar shi sannan ta cire makullin dake kan fuskar wayar, inda daga bisani tayi mishi bincike, wanda a sanadiyyar hakan ne shi kuma ya kashe ta.
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar mummunan lamarin wanda ya faru a ƙauyen Matsapa dake yankin Mutasa dake ƙasar Zimbabwe, inda suka bayyana cewa matar ta mutu a nan take.
‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Muƙaddashin sufeton ‘yan sanda wanda shi ke kula da yankin, Wiseman Chinyoka shine ke kula da yankin, ya tabbatar aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa wanda ake zargi wato mijin matar mai suna Gwaramba Jimu ya arce daga gurin jim kaɗan bayan aikata ta’adin.
Ance gabanin ya arce, sai da yaje ya umurci mahaifiyar shi Kandala Maluwiza mai shekaru 72, da ta kula mishi da yaran shi saboda shi zai bar ƙauyen.
Watansu uku da yin aure
“Ma’auratan dai basu wuce wata uku da yin aure ba. Sun samu matsala ne bayan da Joni ta ɗauki wayar Jimu ba tare da sahalewar sa ba. Bayan sunyi cacar baki a tsakanin su, Jimu yaje ya samu wata antin shin mai suna Netsai Jolomile ‘yar shekara 48 dake ƙauyen Mhandire domin ta sasanta su.
“Jolomile ta rako Jimu zuwa gidan nashi domin ta sasanta su. Ta shawarce su da su yi ƙoƙarin zauna wa lafiya. Daga nan sai ta koma gida ta barsu.
“A ranar 28 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe biyu na dare (2am), mijin, wato Jimu ya tashi sannan ya ɗauka sharɓeɓiyar wuƙa wacce yayi amfani da ita wajen sarar matar tashi Joni a wajen kafaɗun ta, wuyan ta, ƙirji, da kuma bakin ta.” inji muƙaddashin ‘yan sandan.
Ya ƙara da cewa bayan faruwar abun ne Jimu yayi sauri yaje ya faɗa wa mahaifiyar shi Maluwiza akan ta kula mishi da yaran shi, daga nan kuma ya kama gaban shi.
“Maluwiza taji a jikinta cewa wani abu ya faru, sai ta tashi ta tafi gidan ɗan nata, inda isar ta keda wuya sai ta tarar da matar wato Jino kwance cikin jini face-face bata motsi. Daga nan ta sanar da ‘yan ƙauyen, sannan sai aka sanar da ‘yan sanda waɗanda suka garzaya zuwa gurin da abun ya faru.” inji Chinyoka.
Muƙaddashin sufeton ‘yan sandan ya buƙaci ɗaukacin al’umma da su taimaka da bayanin da zai iya taimaka wa wajen kama Jimu.