Labarai

KIRA GA MATAN AURE: Ku daina yi wa mazajen ku kwalelen Jima’i idan suka bukace ku – Likita

Wani kwararren likitan mata Eric Okunna ya bayyana yadda mahimmancin jima’i ga ma’auratan ke taimakawa wajen inganta zaman aure.

A ranar Talata kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta saurari ra’ayoyin mutane a Awka jihar Anambra game da mahimmancin jima’i a aure inda mutanen ke cewa bai kamata ma’aurata na kaurace wa juna ba musamman idan mace ce ke hana mijinta jima’i domin ta hukunta mijinta kan laifin da ya yi mata.

Mutanen sun ce namiji shine babba a gida, mace kuma ke karkashinsa bai kamata ta na hana mijinta samun hutu ta hanyar saduwa ba.

Okunna ya ce jima’i na taimakawa wajen kara dankon soyayya tsakanin mace da miji a aure.

“Jima’i na taimakawa wajen kwantar wa ma’aurata hankalansu tare da kare su daga kamuwa da wasu cututtuka a waje.

Likitan ya yi kira ga mata da su daina hana mazajensu jima’i cewa yin haka na haddasa matsala a aure.

Ya ce akwai hanyoyi da dabaru da dama da mace za ta iya amfani da su domin karkato da hankalin mijinta kan abin da take so amma ba jima’i ba han mijinta jima’i ba.

“Dole ne ma’aurata su samu rashin jituwa a aure sannan jima’i kamata ya yi ya zama dabaran da zai sulhunta mace da mijinta sannan hana miji jima’i na daga cikin matsalolin da ke kashe aure.

Bayan haka Okunna ya gargaddi ma’aurata da kada su mai da jima’i abinci domin yawan bukatan jima’i na iya cutar da lafiyar mace.

“Jima’i na taimakawa wajen kwantar da hankalin mutum inda karancinsa na iya cutar da lafiyar namiji sannan yawan bukatan sa na cutar da lafiyar mace.

A dalilin haka likitan ya ce ya kamata ana sara ana duban bakin gatari.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button