Labarai

Ku Daina Cin Suya, Balango, Tsire, Suna Kawo Cutar Kansa -Likita

Advertisment

Wani masani ilmin kiwon lafiya, Dr. Chinonso Egemba, ya gargadi ‘yan Nijeriya kan cin namar Suya da bai gasu sosai ba saboda hakan kan haifar da cutar Daji (Kansa).

Likitan wanda aka fi sani da ‘Aproko Doctor’ a kafafen ra’ayi da sada zumunta ya yi bayanin cewa akwai sinadarin kemikal dake hawa kan nama idan aka gasa kan hayaki.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Instagram @aproko_doctor, yace idan aka gasa kan hayaki, sinadaran hydrocarbon. Ya ce: Idan ka gasa nama a fili, akwai polycyclic aromatic hydrocarbons ko heterocyclic amines. Wadannan sinadarai na haifar da kwayoyin cuta dake lalata DNA, kuma lalacewar DNA na kai wa ga cutar Daji.”

“Idan kuma aka gasa naman sosai har wasu bakaken gawayi suka hau kan namar, mutum zai fi saurin kamuwa da cutar daji.”

Advertisment

“An gano cutar dajin ciki, mazakura, da mara na da alaka da wadannan sinadarai.”

“Ku tabbatar da cewa duk naman da za ku ci ba gasawa aka yi ba, zaku iya soyawa ko gasawa a cikin oven.”

A cewar sashen ilmin lafiya ta jami’ar Illinois, “Ana samun Polycyclic aromatic hydrocarbon ne idan aka kona abu. Sukan haifar da cutar daji kuma suna illata idanu, koda da hanta.

Sources: legit

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button