Labarai

An yi facaka, an tsine wa kudi, an zabga watanda, an nuna isa da almubazzaranci a bikin zagayowar ranar haihuwar Akpabio, shekaru 61

Advertisment

Duk da tsananini matsin rayuwa da gwamnati mai ci ta jefa ‘yan Najeriya da rana tsaka a kasar nan sanadiyyar cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi, da kuma har yanzu babu wani abu na tallafi kwarara da gwamnati ta bijiro dasu don kawo karshen tsananin talauci da ta jefa mutanen Najeriya ciki, amma kuma sai ga shi shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi wa kudi kisar rashin mutunci a bukin zagayowar ranar haihuwar sa da aka yi a makon jiya.

Idan ba a manta ba tun bayan zanga-zangar da kungiyar kwadago ta yi na nuna fushinta ga halin da gwamnati ta jefa ‘yan Najeriya ciki, da kuma nuna halin ko in kula da take yi na samar da tallafi da yanayin da zai samar wa mutane saukin rauyuwa, gwamnati ta bijiro da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya kyautar naira 35,000 duk wata. Sai dai kuma tunda aka biya ma’aikata a watan Satumba, ba a sake biyan su ba har yanzu abin dai a dofane ya ke, jaridar liberty tvr na wallafa a shafinta.

An yi facaka, an tsine wa kudi, an zabga watanda, an nuna isa da almubazzaranci a bikin zagayowar ranar haihuwar Akpabio, shekaru 61
Convoy din birthday

A jihohi ma shiru ba su ce wa ma’aikatan su komai ba tukunna.

Kasaitaccen bikin da Akpabio ya shirya a takaice dai ba shi misaltuwa sai dai a kamanta bata dan tsakure daga cikin irin watanda da almubazzarancin da aka a wajen shirya wannan biki na kasaita.

Advertisment

Sanatoci da jigajigan ‘yan siyasa sun halarci filin taro na Akwa Ibom domin bikin. Dukkan su sun halarci taron ne a jiragen haya masu daukan mutane kadan, wanda wasu na su ne ma sannan masu dan karan tsada.

Bayan an kammala dabdalar Uyo, an kuma dunguma zuwa Abuja Babban Birnin tarayyara Najeriya inda aka hadu kuma wurin taron domin ci gaba da wannan bikin na cikan Akpabio shekaru 61.

An yi facaka, an tsine wa kudi, and zabga watanda da nuna isa da almubazzaranci a wannan wuraren taruka, kawai domin bikin cikin shugaban majalisar dattawa shekaru 61.

Sai dai kuma hakan ya zo ne a daidai ‘yan Najeriya na ci gaba da dandana wahalar tsananintalauci da halin kakanikayi da suka fada ciki tun bayan cire tallafin man fetur.

Akpabio sananne wajen irin haka, a lokutta da dama tun yana gwamnan Akwa Ibom, ya kan rika yin facaka da kudi wajen shagulgula da bada kyaututtuka ga ‘yan siyasa na babu gaira babu dalili.

Bidiyon zuwansa wajen taro zaku iya kallonsa a Nan

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button