Labarai

Rochas okorocha ya jawo aya alkur’ani mai girma wajen kamfin din shi  ya jawo cece -kuce

Rochas okorocha ya jawo aya alkur'ani mai girma wajen kamfin din shi  ya jawo cece -kuceIdan ba a manta ba, Okorocha ya bayyana ra’ayin sa na takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a wata takarda wacce ya tura wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Yayin jawabin sa, an ga sanatan yana janyo aya daga cikin Al’Qur’ani mai girma inda yace shi dan takara ne mai adalci kamar yadda Allah ya umarci yin adalci cikin Suratul Nahli.
Ya bukaci duk masu sauraron sa da su zabe shi don zai samar da sabuwar Najeriya. Okorocha wanda yanzu haka sanata ne mai wakiltar Imo ta yamma ya sha cece-kuce bayan janyo ayoyin Qur’ani.
Wannan dabi’ce ko dubaru na yan siyasarmu a yau zasu nunawa duniya cewa zasuyi kamfin da addini amma kuma ba addinin ne a zukatansu ba idan ma sun samu gurabunda suke nema to kadan ne ke taimawa addini a cikin shuwagabancinsu.
Ga bidiyon a kasa:


labarunhausa ta tattaro tsokacin da   ‘yan Najeriya bayan bidiyon nasa ya bayyana a Twitter:

babaidris090 ya ce:

“Sai Alhaji Rochas Okorocha, ya zama Sheikh Alrochas bin Okorocha yayin shiga jerin masu takarar shugaban kasa a 2023.”

Aucho00 ya ce:

“Au dama har Rochas so yake yi ya shugabanci Najeriya??”

Franklin_M_F ya ce:

“Ka ba ni damar zama maka matukan jirgin da zaka dinga zirga-ziga a sabuwar Najeriya. Kalli yadda Rochas Okorocha yake jan gemun sa da yatsu kamar shainadin da yake son tara aljanu don su yi masa aiki.”

DareGlintstone tace:

“Rochas ya ko sarki Martin Luther da karfi da yaji. Ba ni zaka yaudara ba.”

iam_leochizzy ya ce:

“Rochas ya ce shi Kyaftin ne wanda zai kai Najeriya sabon wuri. Haka Buhari ya yi mana alkawarin zai canja kasa. Yanzu ga Rochas ya yi. Ko ina zai kai mu oho? Kafin ya kai mu duhu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button