Labarai

Ka Gaggauta Daukar Mataki Akan Abduljabbar Kabara, Sakon Sheikh Lawan Abubakar Triumph Ga Gwamna Ganduje

Advertisment

Fitaccen Malamin addinin musulunci a jihar Kano Sheikh Abubakar Lawan Shuaibu Triumph ya bukaci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya dauki mataki a kan Abduljabbar Nasiru Kabara.
Malamin ya bayyana Abduljabbar Kabara a matsayin mayaudarin mutum matsoraci wanda ya shiga ya fita don kar a zauna da shi.
“Ina daga cikin malaman da suka zauna gaba-da-gaba da gwamnan Kano a kan ya amince a shirya zama da wancan yaron na filin mushe wanda ya zagi Annabi da sahabbansa da matansa a karatukansa ba sau daya ba sau biyu ba da sunan karatu, muna da bayanan yadda wasu jami’an gwamnati suka karbi kudi suka rantse cewa ba za a yi zaman kure yaron ba. Maigirma gwamna idan ba ka sani ba yanzu ka sani muna da tuhuma a cikin gwamnatinka.” Cewar Shehin Malamin.
Ya ce” Dalili na biyu da ke tabbatar da haka shi ne dauke maganar daga hannun kwamishinan addinai zuwa hukumar shari’a wacce ta gama mutuwa a Kano, kenan maganar ba za ta kara tasiri ba. Duk wanda yaji wayar da wannan Yaro Abduljabbar Kabara ya yi da Sheikh Bello Yabo wacce Abduljabbar din ya ke neman a dakko Bello Yabo a zauna da shi za a gane cewa ba son zaman yake ba yaudara ce kawai da hargagi irin nasa don ya san ba zaman za a yi ba, wani shashanci da shirme irin nasa sai ya dinga kiran malamai yana neman su zauna da shi, a cikin azumi wallahi sau uku ina kiransa don ya yarda mu zauna da shi yana kin daukan kirana. Idan da gaske tattaunawar yake so, ni ba na bukatar a saka rana ko lokaci, ko ina kan abun hawa aka kira ni a shirye nake na tattauna ko wace irin mas’ala.” Inji malamin.
“Muna tunatar da Gwamnan Kano cewa musulmin Kano ba su manta da wannan case din ba, kuma wallahi ba zamu manta da shi ba. Yadda ba za mu manta da lamarin rashin tsaro a Najeriya ba, haka ba za mu manta da batun zagin Annabi a zauna lafiya ba. Kuma a wayance zuwa gaba gwamnati za ta bude masa masallacin da yake zagin Annabi da sahabbansa da matansa, ga shi nan ana sanarwa a Facebook a kawo masa ziyara a rana kaza, mutane na haduwa a gidansa ana bidiyo da hotuna ana watsawa, wannan ya zama wasan kwaiwayo da shirita, in da gaske gwamnati tana son a gama da wannan lamari, shi yana zargin cutar sa aka yi aka rufe masa masallaci, mu kuma muna zargin addininmu ya cutar ya ci mutuncin Annabinmu da matansa da sahabbansa sai gwamnati ta zaunar da mu mu tattauna wanda hukunci ya tabbata a kansa a zartar masa, idan ya tabbata mu ne makaryata a zartar mana da hukunci kar mu sake magana a kansa, idan ta tabbata abin da muke fada ya zagi annabi a yi masa hukunci irin na wanda ya zagi a Annabi a kama shi a daure shi.”
“Kuma cewar da ake mu zauna da shi sau nawa muka kira shi ya ki, dama karya yake ba zai zauna ba, abin da ya sa muke son gwamnati ta shiga shi ne dukkanmu a kasanta muke za ta kira mu ta kuma kira shi. Idan muka ce mu da shi za mu zauna yana da mutanen da zai zo da su mu ma muna da su watakila abun ya zama hayaniya. Amma a kira mu ofishin DSS mana ko na kwamishinan ‘yan sanda ko fadar gwamnati daga mu sai shi sai a yi bidiyo kowa ya gani.”-Malam Lawan Abubakar Triumph.
Idan ba a manta ba, gwamnatin Kano ta zartar da matakin rufe masallacin Abduljabbar Kabara tare da hana shi karatu bisa kiraye-kiraye da aka yi mata na zargin samun Abduljabbar Kabara da aikata batanci ga janabin Annabi (S.A.W.) da zagin sahabbansa da matansa da magabata na kwarai da kuma karyata Alqur’ani da azabar kabari da tashi daga cikinsa, kungiyar Izala, Tijjaniya da Qadiriyya sun bayyana godiyarsu ga matakin gwamnatin Kano, matakin da Abduljabbar Kabara ya ce ba a masa adalci ba.
Daga Indabawa Aliyu Imam

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button