Labarai

Kaji Abinda Sarkin Musulmi Yace Kan Badaƙalar Gidan Abuja !!!


A karon farko Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar III CFR, mni, ya yi magana kan Badakalar gidan Abuja da aka alakanta shi da ita.

Sarkin Musulmi yace “Ina tunanin akwai wani mutum a wani wuri dake son lalatamin suna ni da Gwamnan Sokoto. Idan ba haka ba; banga dalilin bayarda labarin Gwamnatin jihar Sokoto ta saima Sarkin Musulmi gida a Abuja ba, wanda ke da gida a can tun kafin wannan. Ina mamakin yadda ake aikin Jaridanci a yanzu. ‘Yan jarida suna kutsawa cikin al-amurran da basu da masaniya, basu san yadda labari ya fara ba da kuma yadda zai kare, amma sai su rubuta labarin su buga shi. Wannan na daga cikin matsalolin Kafafen Sadarwa na Zamani (Social Media)”
“Gaskiyar abinda ya faru shine, Gwamnatin jihar Sokoto ta yanke shawarar sayen gida a Abuja domin Majalisar Sarkin Musulmi amma ba don Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar III ba; gidan dai za’a rika amfani da shi ga duk wanda ya zama Sarkin Musulmi, shine gaskiyar labari. Bayan da suka zauna taron Majalisar Zartarwar jaha suka tattauna lamarin kuma suka aminta, anyi abin bisa ka’ida. Duk mu’amalar da akayi kan gidan da aka son saya a Abuja, gwamnati ce ta yi. A lokacin da suka tuntube ni kan gidan na Abuja, suka ce min suna son sayen gida tare da sanya masa kayayyaki na kimanin Naira Biliyan Daya (N1 Billion), sai nace da su Aa; Me yasa za’a saima Majalisar Sarkin Musulmi gidan sama da Biliyan Daya, zan fitarda dukkanin kayayyakin dake gidan da nike ciki yanzu, zuwa wannan sabon gidan na Majalisa”.


“A kan haka ne babu bukatar gwamnati ta sanya kayayyaki cikin gidan, kudin sayen gidan ya rage zuwa Naira Biliyan Daya zuwa Miliyan Dari Shida da Hamsin (N1 Billion to 650 Million). Wannan abin yabawa ne ga kowa, amma saboda an biya kudin sayen gidan daga asusun gwamnati zuwa asusun wani dan asalin jaha wanda ke harkokin sa na kasuwanci, da damar yin kasuwanci, kuma yayi ta yiwa gwamnati Kwangila domin shi ba ma’aikaci bane, wani mutum daga Hukumar EFCC wanda ke da ikon hakan, ya bada bayanin lamarin. Amma bayan da suka ga dukkan lamarin, sun fahimci babu wani rashin gaskiya a tsarin fitarwa da sanya kudin da akayi. Amma wani daga Hukumar ta EFCC ya bada labarin ga wata jaridar yanar gizo, waanda suka rubuta cewa; Ina da gida a Abuja kuma na karbi Kudi ga gwamnati domin sayen wani gidan. Abin da ban dariya”
Sarkin Musulmi ya kara da cewa “A ko yaushe ina farin cikin duk na tuna cewa wadannan mutanen da suka yi min haka taimako na ne suke, domin kuwa Allah zai kankare zunubbai na ya sanya musu su. Abinda Allah yake yiwa wadanda suke irin wannan munafucci shine, zai dauke ayukkan su na kwarai ya musanya su da zunubban wanda suka yiwa ba dai-dai ba. Shi yasa naki yin magana kan lamarin, kuma ba zanyi ba, domin hakan a wurina ba dai-dai ba ne.

Gaskiya a bude take ga kowa, ba wani bin rashin ka’ida da aka aikata, kuma Gwamnatinjihar Sokoto ta fitarda hujjoji, shi kenan. Kuma ka san har yanzu, gwamnati ba ta hannunta gidan na Abuja ba Majalisar Sarkin Musulmi, wanda ni zan sanya masa kayayyaki da kudi na. Sune zasu sayi gida, amma da zaran sun kammala cinikin zasu bayarda shi ga majalisa. Kuma zamuyi duk yadda ya kamata domin tabbatar da gidan ya samu kulawar da ta dace, tare da yin tarukkanmu a ciki, da karbar bakinmu a ciki ba tare da mun yi aron dakunan taro domin yin tarukkan mu ba.

Wasu ‘yan asalin Sokoto da suka yi magana da wakilin kan gidan na Abuja, sun sheda masa cewa an dauki nauyi wasu ne kawai domin batawa Sarkin Musulmi suna.

MADOGARA: Jaridar Vanguard

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button