Labarai

Ba zamu yarda Tinubu ya dauki Musulmi matsayin abokin tafiyarsa ba, Babachir Lawal

Abuja – Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa ba zai yiwu Tinubu ya dauki wani Musulmi matsayin mataimakinsa ba a zaben 2023.

Babachir ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Seun Okinbaloye na ChannelsTV.

Ya ce sam ba zai yiwu wani yayi tunanin tikitin Musulmi da Musulmi ba dubi ga yadda lamarin siyasar Najeriya yake.

Yace:

Za ku iya samun yan takara masu kyau amma idan baku ci zabe ba, bacin lokaci ne. Saboda haka mu sani cewa duk wanda aka zaba mataimaki zai taimaka wajen nasara a zabe.”

Kan Shawarar tikitin Musulmi-Musulmi, cikin Kiristoci nike rayuwa kuma na san ba zasu yarda da lamarin nan ba.”

“Buhari shi kansa a baya sai da ya ajiye dan takaran yanzu saboda dukkansu Musulmai ne.”

Babachir yace akwai bukatar jam’iyyar tayi nazari da kyau kafin zaben wanda zai yiwa Tinubu mataimaki.

Rabuwar kai tsakanin addinai da kabilu ya karu. Kawai APC ta zabi Kirista mataimaki saboda mun san abinda PDP za tayi kenan.”

Madogara: Legit

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button