Kannywood

“Mu ‘Yan Fim, ba Jahilai ba ne”–Ummi Abdulwahab

Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywwod Ummi Abdulwahab, wacce aka fi sani da Ummi El-Abdul ta bayyana cewar su Yan fim ba Jahilai ba ne, su na da ilimin su daidai gwargwado shi ya sa ma su ke yi fadakarwa a cikin sana’ar su ta fim.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Wakilin Jaridar Dimukaradiyya Kan irin kallon da a ke yi musu na cewar ba su da ilimi shi ya sa su ke yin abin da suna ga dama.
“Mu ‘Yan Fim, ba Jahilai ba ne”–Ummi Abdulwahab
Ummi ta ce “Ai shi ilimi ba ya buya Kuma ana gani a cikin sana’ar da mu ke yi, don haka mu ba Jahilai ba ne muna da ilimin mu, don haka a daina yi mana kallon Jahilai”
Ta Kara da cewar “kowa da ka gani da yadda Allah ya tsara masa rayuwar sa to mu ma haka rayuwar mu ta kasance, Kuma yanzu da na ke yin harkar fim idan Allah ya kawo mini miji na yi aure shikenan sai dai a rinka labarin na taba yin fim a baya.”

Daga karshe ta yi fatan Allah ya sa ta gama da harkar fim lafiya ta samu miji ta yi aure.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button