Wakilan Yahudawa Masu Rusa Tarbiyyan Musulmi – Datti Assalafy
Martanin Datti Assalafy ga Umma Shehu Akan kalubalantar Da tayiwa Hukumar hizbah da ta kama Sadiya Haruna kan hotunan tsiraici
Kamfanin jaridar Dokin Karfe TV sun daura bidiyo na wannan fitsararriyar yarinya Umma Shehu wacce take sana’ar wasan kwaikwayo a masana’antar Hausa film
Umma Shehu tayi mummunan suka wa rundinar Hisbah na jihar Kano sakamakon Hisba ta cafke kawarta fitsararriyar yarinya Sadiya Haruna a dalilin yada hotunan batsa da kalamai na batsa da Sadiya Harunan takeyi a shafikanta na sada zumunta
Shine wannan yarinya marar kunya wacce bata da tarbiyya ta yi bidiyo tana tuki a cikin mota taci mutuncin rundinar Hisbah na jihar Kano, har tana kokarin yiwa shugabannin Hisbah sharri kamar yadda artificial karuwai na wannan zamanin suke sharri domin aji tsoron su.
A maganganun da Umma Shehu tayi tace Hisba su saki kawarta Sadiya Haruna, wai a bar Sadiya tayi iskancinta yadda ta ga dama, har tace suma ma’aikatan Hisba din akwai masu neman mata a cikinsu, zata iya tona asiri, don haka Hisbah su kyale Sadiya tayi abinda ta ga dama, ko yawo tsirara zatayi a barta tana da ‘yanci
Jama’ar Musulmi wadannan sune fa wai suke sana’ar Hausa film wasan kwaikwayo da sunan suna bada tarbiyyah wa Musulmin Kasar hausa, imba jahilci ba waye zaiyi wannan maganar alhali yana dan Musulmi? ko da yake ba abin mamaki bane, na tuna hiran da Sheriff Momoh yayi da wannan yarinya aka tambayeta izu nawa ake dashi a Qur’ani? tace bata sani ba
Maganganun da wannan fitsararriyar yarinya tayi akan Hisbah ko wanda ba Musulmi bane yayi, za’ace yayi karshen rashin kunya da fitsara da rashin ladabi wa rundinar Musulunci da take kokarin kare shari’ar Allah
Maganganun Umma Shehu yayi kama da na ‘yan “Interfaith”, wani sabon addini ne daga cikin rassan addinin “Atheism” wadanda suke da’awar babu Allah, ayi watsi da addini, abar kowa ya aikata abinda ya ga dama kamar rayuwan dabbobi a gandun daji
Ya kamata Hisbah su kama wannan yarinya su kwabi bakinta duk ranar da ta taka kafarta a Kano, taje duk inda taga dama tayi iskanci da fitsara duniya ta isheta, amma banda garin Kano cibiyar Musulunci
Muna son Kano, muna kaunar Kano, duk abinda ya taba Kano ya taba Arewa, don haka muna goyon bayan Hisba dari bisa dari, lallai ku dage sosai wajen yaki da karuwai na karshen zamani masu lalata tarbiyyan al’ummah
Yaa Allah Ka tsare Musulunci da Musulmai daga sharrin karuwan karshen zamani