Kannywood

Bidiyon Jarumi Adam Zango tare da Muneerat Lumansi mai koyar da kwanciyar aure ya tayar da kura

Wani bidiyo wanda ya bayyana inda aka ga Jarumi Adam A Zango, tare da Muneerat Abdulsalam wacce aka fi sani da Lumansi su na tikar rawa ya janyo cece-kuce.
Mutane da dama su na yabon jarumin tare da yabawa da halayensa tun bayan bayyanar labarin daukar nauyin karatun marayu fiye da 100 da ya yi a Zaria, cikin jihar Kaduna.

Bidiyon Jarumi Adam Zango tare da Muneerat Lumansi mai koyar da kwanciyar aure ya tayar da kura
Bidiyon Adam Zango tare da Muneerat Lumansi mai koyar da kwanciyar aure ya tayar da kura
 

Lokacin mutane su ka dinga musanta batun yayin da wasu suke ta yaba masa.
Sannan kuma ana matukar ganin darajar jarumin bisa taimakon da yake yi wa abokan sana’arsa idan sun shiga cikin matsala, wanda hakan ya ke matukar kankaro masa girma, kima da mutunci a idon duniya duk da kasancewarsa mawaki kuma shirin fim din hausa.
Sai dai a bangaren Muneerat Abdulsalam wacce aka fi sani da Lumansi ba haka bane. Don mutane da dama ba sa ganin mutuncinta a kafafen sada zumunta saboda yadda take bayyanar da dukiyar fulaninta a waje yayin yin bidiyoyi.
Sannan ta na bayyana a YouTube da Facebook ta na koyar da kwanciyar aure babu kunya balle tsoron.
A shekarar da ta gabata ma har bayyana ta yi a wani bidiyo inda ta ce ta bar musulunci, wanda hakan ya yi matukar tayar da kura.
Bayyanar mutane biyun mabanbanta tare ya matukar razana mutane, kamar a ga dan malam da diyar boka ne.
Duk da dai ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba, amma muna fatan Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe ya kuma bamu zuri’a tsarkakakkiya, Ameen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button