Kannywood

Shirin ‘Nih’lah’ zai kawo sauyi a Kannywood kamar yadda mu ka yi da ‘Sarki Jatau’ – Barde

BABBAN furodusan wani sabon fim da zai fito a wannan makon mai suna ‘Nih’lah’, Alhaji Habibu Barde Muhammad, ya bugi ƙirjin cewar shirin zai yi matuƙar kawo gyara a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood.

Ya ce gyaran zai zo ne ta fuskar rashin tsari da kuma yadda ake shigowa masana’antar ba bisa ƙa’ida ba.

A hirar sa da mujallar Fim, Barde ya ce ya zo da hanyoyi na yadda za a fuskanci matsalar da ta ke sawa ake shigowa masana’antar ta-ci-barkatai.

Ya ce, “Don haka ne na kashe kuɗi masu yawan gaske domin bada tawa gudunmawar don ganin an ceto harkar daga lalacewa.”

Furodusan ya ƙara da cewa, “Duk da cewar ana ganin kamar harkar fim ta mutu, to ni ina ganin idan har ka yi abu na ƙwarai, to har gida za a zo a same ka a saya.

“Don haka, kamar yadda mu ka saba zuba kuɗi mu na yin fim mai inganci a baya, shi ya sa ma a wannan lokacin ban karaya ba.

“Domin kowa ya san fim ɗin da mu ka yi, ‘Sarki Jatau’, to da yake mun kashe kuɗi mun yi abu mai inganci, har yanzu mu na cin gajiyar sa.

“Domin haka za mu ci gaba da yin finafinai masu inganci; ko da ba mu samu wani abu na riba a yanzu ba, za mu samu nan gaba.”

Shi dai wannan fim ɗin na ‘Nih’lah’, Ahmad Bifa ne daraktan sa.

Za a fara haska shi a gidan sinima na ‘Film House’ da ke Ado Bayero Mall, Kano, a ranar Juma’a mai zuwa, 10 ga Janairu, 2020.

Za a shafe tsawon kwanaki ana haskawar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button