Kannywood

Mummunan zato mutane su ke yi wa harkar Fim ~ Cewar Karimar Izzar so

Khadija Yo izzaSo

Mummunan zato mutane su ke yi wa harkar Fim, inji Karimar Izzar so

Fitacciyar Jarumar Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karima, a cikin fim din Izzar so. Ta bayyana harkar fim a matsayin hanyar fadakar da jama’a, da kuma sana’ar da ta ke samar da abin rufin asiri ga masu yin ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da wakilin jaridar Dimokuradiyya, dangane da yadda a ke yi musu kallon mutanen da su ke bata tarbiyyar Matasa, in da ta ke cewa.

Khadija Yobe wanda anka fi sani da karima izzar so

“To gaskiya ba haka ba ne, mutane ne su ke yi wa harkar mummunan zato, kuma shi mummunan zato haramun ne, don haka ya kamata mutane su rinka yi wa harkar fim adalci.”

Jarumar ta cigaba da cewar “Ni tun da na shiga harkar fim, babban buri na shi ne na zama ina fadakar da jama’a, ta hanyar isar da sakon da ya ke cikin fim, kuma ya zamar mun, wata sana’ar da za ta rufa mini asiri, don idan mutum ya kiyaye mutuncin sa, to zai ci ribar sana’ar fim, don haka na ke fatan na samu ribar da take cikin sana’ar fim din. ” Inji ta.

KARANTA WANNAN LABARIN:

Ruwan Nono na Jarirai ne Ku dena Bawa Mazajenku’, Kwamishina ta Shawarci Iyaye mata

Babban Burina A Duniya Nayi Aure – Jaruma Fati Yola

Da muka tambaye ta, dangane da yadda matan da su ka daukaka a fim, su ke ganin sun fi karfin aure kuwa, cewa ta yi.

” To ni ina ganin ba haka ba ne, domin shi aure lokaci ne, idan lokacin ya zo babu yadda za ka yi, kuma, don haka ni ina da burin ko me na ke yi idan Allah ya kawo mini miji nagari zan yi aure, wanda zai kare mun mutuncina, da na ya’yana, amma ni ba na kallon kudin mutum, ko wani abu da ya mallaka.” a cewar ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button