Jarumi Ali Nuhu ya Zama Gwamnan jihar Kogi a wani Shirin film Mai suna The White Lion
Shahararran jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya samu damar hawa matsayin gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a cikin wani fim ɗin Nollywood da ake ɗauka yanzu.
Shirin, mai suna ‘The White Lion’, ana shirya shi ne a garin Lokoja domin nuna irin gudunmawar da gwamnan ya bayar ga al’ummar jihar sa, musamman matasa da kuma ɓangaren harkokin siyasa.
Wasu ‘yan Nollywood ne ke shirya fim ɗin da harshen Turanci.
Daraktan shirin shi ne Tunde Olaoye, wanda fitaccen mai bada umarni ne a Nijeriya. Ya yi daraktin finafinai da dama, kamar su ‘Bosun’s Empire’, ‘Lugard’, da kuma ‘Fools’ Day’, wanda zai fito a ranar 24 ga wannan watan na Satumba.
Ɗaya daga cikin manyan jaruman shirin na ‘The White Lion’ ita ce fitacciyar jarumar Nollywood ɗin nan, Roseanne Chikwendu, wadda ake ɗauka a matsayin matar gwamnan Kogi, wato Rashidat Yahaya Bello.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Alhaji Yahaya Bello na daga cikin gwamnonin Arewa da ake raɗe-raɗin za su nemi takarar shugabancin ƙasar nan a shekarar 2023.
Akwai hasashen cewa shirin ‘The White Lion’ wani ɓangare ne na tallafa wa burin gwamnan na zama shugaban ƙasa.
Roseanne Chikwendu a matsayin Rashidat Yahaya Bello a shirin ‘The White Lion’
Ali ya taɓa yin iƙirarin cewa wasu jaruman finafinan Hausa su ma su na da ƙudirin tsayawa takara a zaɓen ƙasar nan da ke tafe a cikin 2023.