Kannywood
Yanzu-yanzu : Allah yayi wa Darakta Aminu S Bono Rasuwa


Advertisment
Yanzu nan Majiyarmu ta samu wani babban rashi da masana’atar kannywood tayi wanda tayi rashin mai bada umurnin wato darakta aminu s bono rasuwa.
Sanarwa ta fito daga shugaban hukumar tace fina finai a jihar Kano Abba Elmustapha da ya wallafa a shafin na sada zumunta kamar haka.
“INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN
Allah Yayiwa Shahararren Darakta a Masana’antarmu Kannywood AMINU S BONO Rasuwa.
Muna Addu’ar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Kurakuransa Yasa Aljanna Ce Makomarsa. Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani.”
Za A Yi Jana’izarsa Gobe Da Safe A Unguwar Su Ta Dandago Dake Birnin Kano, Da Misalin Karfe Tara Na Safe.