Kannywood

Kwamandan Hisbah Ya Bayyana Abinda Yasa Suke Neman Umma Shehu

Abin da Yasa Hisbah ke Neman Umma shehu ~ Harun Sani Ibn Sina

Advertisment

Abin da Yasa Hisbah ke Neman Umma shehu ~ Harun Sani Ibn Sina
Abin da Yasa Hisbah ke Neman Umma shehu ~ Harun Sani Ibn Sina
Hoto :Instagram
Daga :bbchausa

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce tana gayyatar tauraruwar fina-finan Kannywood, ummahshehu , domin ta yi mata karin bayani bisa zargin da ta yi wa wasu jami’anta.
.
Babban Kwamandan rundunar, Harun Sani Ibn Sina, ya shaida wa BBC Hausa suna neman tauraruwar ne bayan da ta yi zargin cewa jami’an Hisbah suna aikata laifuka amma sun ki duba nasu suna takurawa talakawa marasa galihu.
.
Wasu rahotanni sun ambato tauraruwar tana yin raddi ga hukumar Hisbah bayan da ta kama kama wata ƴar wasan Kannywood da kuma ta yi fice a kafar sada zumunta, Sadiya Haruna, kan “yaɗa hotunan batsa” a shafukanta na sada zumunta.
 
Rahotannin sun nuna cewa Ummah Shehu ta fusata matuka kan matakin da Hisbah ta dauka inda ta yi zargin cewa hukumar ta fi mayar da hankali wajen hukunta talakawa da ‘yan fim bayan kuwa masu hannu da shuni da kuma jami’an hukumar suna tafka ta’asa ba tare da an yi musu hukunci ba.
.
Sai dai mun yi yunkurin jin karin bayani daga gare ta amma ba ta amsa kiran wayar da muka yi mata ba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button