Labarai

‘Ruwan Nono na Jarirai ne Ku dena Bawa Mazajenku’, Kwamishina ta Shawarci Iyaye mata

Kwamishinan al’amuran jinsi ta jihar Enugu, Hon. Peace Nnaji na son mata su dena “Shayar da mazajensu” tare da ajiye ruwan nonon ga jariransu.
Kwamishinar ta yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa da manema labarai da UNICEF ta shirya.
Kamar yadda Jaridar Prime Times hausa na ruwaia. Ta yi bayanin cewa ba dai-dai bane maza su dinga shan maman matayensu inda ta ce an yi ruwan nono domin jarirai ba mazaje ba.
“Ruwan nono na jarirai ne ba na iyaye maza ba. Yakamata iyaye mata su dena shayar da mazajensu da ruwan mama na jariransu ne.
” Ba dai-dai bane iyaye mata su dinga kaucewa shayar da jariransu saboda tsoron kar mamansu ya zube”.
Kwamishinan ta kuma shawarci iyaye mata da su dinga shayar da jariransu har zuwa watanni 6 domin inganta lafiyarsu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA