Wasu Matasa Mabiya Abduljabar sun Bar tafiyarsa Bayan Gaskiya ta bayyana A Jiya (Hotuna)
A cikin wannan postin namu zaku ga wasu zaratan matasa da sunka nuna cewa tabbas malaminsu yakasa amsa tamboyinda ankayi masa sun daina binsa maana sun bar tafiyarsa.
Ga matasana kamar haka na farko yana mai cewa.
“Ni Abdulrashid Sani daga yau na barranta da malam Abduljabbar da kuma kungiyar sa akan wannan mukabalar, a magana ta gaskiya na so ace malam Abduljabbar yafi abokan karawar sa gaskiya, to amma sai naga sa6anin hakan, ita kuma gaskiya daya ce daga kinta sai 6ata.
Mai magana yana cewa:
انظر لذات القول لا للقائل # فالحق مقبول ولو من جاهل
Kayi duba ga zatin magana(hakikar abun da ake fada) ba wai mai maganar ba, domin ita gaskiya abar karba ce ko da daga jahili take.
Saboda haka ni na karbi wannan gaskiyar. ALLAH YA KARA NUNA MANA GASKIYA YA BAMU IKON BIN TA A DUK INDA TAKE.”

Sauran ragowar zaku gansu a cikin hotuna masu dauke da rubutu.










