Addini

Dr Jabir sani Maihula Yayi Martani Kan mukabalar da Ankayi tsakanin Abduljabar Da Malaman kano

A yau din nan ne babban shehim malamin addinin musulunci as sheikh dr jabir sani mai hula Sokoto akan mukabala da ankayi tsakanin Abduljabar Nasiru kabara da malaman kano a jiya 10/07/2021 kamar yadda gwamnatin kano ta sanya.
Wanda kuma alhamdulillahi anyi mukabala an tashi lafiya lau shine dr jabir sani mai hula yayi martani da kalamai masu hikima akan wannan mukabala da ta gabata ga abinda yake cewa :

Tun kafin Mukabala, duk mai ilimi ko mai hankali ya san abubuwan da AbdulJabbari ke fadi ba gaskiya bane. Bayan Mukabala kuwa babban darasin da yakamata mu dauka shine, Allah Yana karya mai fariya domin Allah baya son mai fariya. Ko Makanike kake idan kana fariya kana nuna kafi kowa sai Allah Ya nuna maka kai ba kowa bane. Idan kana ganin kana da wata baiwa, kamata yayi ka godewa Allah akai, ba kayi fariya da cika baki ba.
Bayan dadi da naji cewa mabiyansa zasu gane ba akan gaskiya yake ba, kuma ya bani tausayi gaskiya; kamar shugaban kasa ne da akayiwa juyin mulki ko mai kudi da talauce fa. Allah Ya sa ya tuba. Masoyanshi na gaskiya cikin mabiyansa zasu bashi shawara.
Allah Yasa mufi karfin zukatanmu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button