Ita dai daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 kenan tana gudana.
Wanda ya fara kafa ta kuwa shine Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.
Mallam Aminu Ibrahim Daurawa wanda fitaccen malamin addinin musulunci ne a Najeriya ya shaidawa BBC cewa abubuwan da ake jinginawa Manzon Allah waɗanda aka same su a ƙasar Turkiyya ya faru ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.
Wani sarki a lokacin yaƙin duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta’addanci, don haka wannan sarki yasa aka tara sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu dake da alaƙa da Manzon Allah don kada a maimaita ƙona alkyabbar Manzon Allah da Magul suka yi a Bagadaza.
Malamin ya ce shi yasa duk wani abu da ake jinginawa Manzon Allah sai aka kwashe su aka mayar da su Turkiyya domin samun kulawa ta musamman, d akuma kare su daga sharrin kafirai.
Gashin gemun Annabi Muhammad, da Hatiminsa da wasikunsa, da takubban Annabi Muhammad da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga dumin masoya Annabi Muhammad na duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alakantawa da sh