Ina Mamakin masu Cewa Abduljabbar yana Zagin Sahabbai?
Ya kamata fa kowa ya sani, Nigeria ƙasa ce da ba ruwanta da Addini, don haka dokar ƙasa ta ba da kowa damar ya yi Addininsa yadda yake so, bisa yadda ya fahimta. Don haka kar kowa ya tsangwami Aduljabbar a kan ra’ayoyinsa da yake bayyana su a kullum, ko da sun cika da zagin Sahabbai, da ƙaryata Sunna hujjar Muslunci, da zagin magabata da sauran manyan Malaman Addinin Muslunci.
Ai shi Abduljabbar gaskiya yake faɗa, daga littatafan Hadisi yake cirowa. Kuma waɗanda ake cewa su ne Malamai in sun isa su musa.
Wannar ita ce hujjar Abduljabbar da yaransa, a kan abin da yake yi na zagin Sahabbai, da koya wa matasa keta alfarmar Hujjojin Addinin Muslunci, da cin zarafin manyan mutane a cikin al’ummar Musulmi, tun daga kan abokan Annabi (saw) da sarakanansa kuma khalifofinsa, da matansa da ƴaƴansa da masu yi masa hidima da sauran almajiransa har zuwa kan Tabi’ai, mabiyansu, zuwa kan na bayansu Limaman Addini, har zuwa kan Malaman Muslunci na kowane ƙarni har zuwa wannan zamani.
To mutane da yawa in sun tashi a kan wannan kawai suke tsayawa, alhali lamarin Abduljabbar ya girmama, ya faɗaɗa, ya tumbatsa har ya wuce wannan, ya isa kan jagoran al’ummar gaba ɗaya. Kai, shugaban ƴan-adam gaba ɗaya, wato Annabi Muhammadu Manzon Allah (saw).
Mutumin da yake danganta munanan maganganu da ƙazaman aiyukan assha ga Annabi (saw), yake keta mutuncinsa, yake yaga alfarmarsa, yake zubar da ƙimarsa, yake danganta masa Fyaɗe da makamantansa!
To in a dokar ƙasa babu laifi ka ci mutuncin Annabi (saw), to a dokar Muslunci wannan kafirci ne da zandaƙa, da yaƙi da Allah da Manzonsa da dukkan al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
Kai idan dokar ƙasa ita ce Addininka, to ka dena alaƙanta kanka da Muslunci, don a Muslunci idan ka faɗi kalmar Kafirci sunanka Kafiri, wanda ya wajaba kotun Shari’ar Muslunci ta tsayar maka da haddin ridda. Allah ya ce:
{وَلَقَدْ قَالُوا كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُوا بَعْدَ إِسْلَامِهِمْ} [التوبة: 74]
Kalma ɗaya da dokar ƙasa ta ba ka dama ka faɗa, a Muslunci idan ka faɗe ta sunanka Kafiri wanda ya wajaba a tsayar maka da hukuncin kisa.
Ni a iya sanina, duk cikin Kafirai da Munafukai da Zindiƙai na da da na yanzu masu zagin Annabi (saw) ban taɓa jin wanda ya danganta Fyaɗe ga Annabi (saw) ba sai Abduljabbar da wani Malaminsa ɗan Ƙala-ƙato mai suna: Ahmad Subhiy Mansur, wani ɗan ƙasar Misra, wanda ya ci mutuncin Annabi (saw) a cikin Littafinsa mai suna: “القرآن وكفى مصدرا للتشريع الإسلامي” irin yadda Abduljabbar yake yi kakal da kakal, iri ɗaya sak, daga wajensa Abduljabbar ya kwafo cin mutuncin Annabi (saw) yake yi, ta hanyar danganta alfasha gare shi da Hadisin Ummu Haramin da Hadisin Jauniyya, wanda a kansa ya danganta kalmar “FYAƊE” ƙarara ga Annabi (saw) inda yake cewa:
“إنه حاول اغتصاب امرأة أجنبية جيء له بها، وأنها رفضته وشتمته باحتقار…، ونفهم من القصة أنها مخطوفة، جيء بها رغم أنفها”.
القرآن وكفى مصدرا للتشريع الإسلامي (ص: 119)
Yake danganta wa Annabi (saw) cewa -wai-:
“Ya yi ƙoƙarin FYAƊE ga wata mace, wacce aka zo masa da ita, alhali ita kuma ta ƙi shi, ta zage shi cikin wulaƙantarwa…., kuma za mu fahimta daga ƙissar cewa; ita matar kidnapping ɗinta aka yi, aka zo da ita bisa tilastawa”.
Ka koma baya, ka fara karantawa daga shafi na 115 zuwa shafi na 119, inda ya yi magana kan Hadisin Ummu Haramin da Hadisin Jauniyya, za ka ga sak duka irin kalmomin da ya faɗa su Abduljabbar ya kwafo yake fassarawa da Hausa, yake zagin Manzon Allah (saw) a tsakiyar al’ummar Musulmi, yake cin mutuncinsa, ba don komai ba, sai don ya zubar da ƙimar Littafin Sahihul Bukhari, littafin da shi ne na biyu a cikin Addinin Muslunci gaba ɗaya kakaf. Saboda idan aka rusa wannan littafi, to duka na bayansa ma sun rushe. Kuma da ma su ne littatafan kafa hujja a Muslunci, daga Alƙur’ani sai Sahihul Bukhari, daga sun rushe to ka ga an rushe bayanin Alƙur’ani, shi kenan sai ya zama an rusa haƙiƙanin Muslunci.
Wannan ya sa nake mamakin mutane idan suka taƙaita suka ce: Abduljabbar yana zagin Sahabbai, kamata ya yi su ce: Abduljabbar yana zagin Annabi (saw), zagin da duk Duniya su biyu ne kaɗai suka taɓa yin irinsa ga Annabi (saw), alhali babu zagi sama da shi.
Wannan shi ne hoton wannan Zindiƙi, Malamin Abduljabbar wajen danganta ma Annabi (saw) Fyaɗe da Alfasha
Rubutawa : Sheikh Aliyu Muhammad sani