Addini
Tsarabar Juma’a: Dalilin da ya sa muka rasa kwanciyar hankali a rayuwa – Dakta Ahmad Ibrahim BUK
Advertisment
A wa’azin da gidan Rediyon DALA FM ke sa wa kowacce safiya na Malamin Hadisi Dakta Ahmad Ibrahim BUK, a safiyar Larabar da ta gabata ya yi jan hankali ne bisa dalilin da ya hana mu samun kwanciyar hankali.
“Dalilin da ya sa muke shan wahala a rayuwa shine mun dauka kudi shine maganin kowacce matsala a rayuwa. Shi ya sa idan muka rasa su sai mu shiga matsala. Mun dauke su da matukar muhimmanci da idan muka ga mai kudi sai mu yi kamar mu bauta masa.
Abinda ba mu sani ba shine shi kudi ba shine maganin kowacce matsala ba, wani bangare ne na jin dadin rayuwa. Arziki ne kuma ba shi kadai ne arziki ba. Ba wai iyu ka ga Allah Ya hadawa mutum komai na rayuwa a duniya ba. Idan ya ba shi kudi kai ma akwai wani arziki da Allah Ya ba ka.
Shin Lafiya ba arziki ba ne? Ilimi ba arziki ba ne? Kyau ba arziki ba ne? Maikudi zai iya rasa lafiya kai Allah Ya ba ka. Maikudi zai iya samun ‘ya’ya su kangare masa Allah Ya Shirya maka naka. Duk abinda Allah Ya ba ka da za ka iya amfani da shi arziki ne. Sana’ar ka idan ka yarda da Allah ka yarda da ita sai Allah Ya daukaka ka a cikin ta.
@alummata
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com