Lauyoyi na sun yi mun shigo-shigo ba zurfi – Malam Abduljabbar


Malam Abduljabbar Kabara ya zargi lauyoyin sa da yi masa shigo-shigo ba zurfi.
Malamin ya bayyana hakan a gaban kotu, bayan da lauyoyin sa suka bayyana janyewar su daga bashi kariya a kotu.
Freedom Fm ta ruwaito ,ya ce, lauyoyin sa su ne suka hana shi magana a baya, duk da cewa yana son yin magana, har ta kai ga kotu ta ce a gwada lafiyar ƙwaƙwalwar sa.
Abduljabbar ya kuma ce, a yanzu lauyoyin sun gudu sun bar shi, sakamakon yadda yaƙi amincewa da buƙatar su na amsa cewa shi mahaukaci ne a gaban kotu don ya kuɓuta.
Tuni dai kotu ta bashi damar sake ɗaukar lauya domin ci gaba da kare shi.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


