Banda Uban Gida A Kannywood Nine Uban Gidan Kaina ~ Yakubu Muhammad
Daya daga cikin fitattun masu shirya fina-finan Hausa kuma mawaki a Najeriya Yakubu Mohammed ya ce har gobe yana jam’iyyar PDP.
Jarumin ya bayyana haka ne a hirar da BBC ta yi da shi a Instagram ranar Laraba, inda ya ya tabo batutuwa da dama da suka shafi nasarorinsa a harakarsa ta fim da waka da kuma alakarsa da abokan sana’arsa.
Yakubu Mohammed ya ce tun da ya fara siyasa jam’iyyar PDP yake goyon baya. “Tun farko da ita na fara kuma har yanzu ina PDP,” in ji shi.
Ya kare dalilinsa na goyon bayan jam’iyyar mai hamayya a Najeriya inda ya ce sun yi wa jam’iyyar ayyuka da dama, wanda shi ne ya ja ra’ayinsa, kuma ita ce uwar siyasa kuma tsohuwar jam’iyya, a cewarsa.
tar mata a fina-finan Nollywood – Ali Nuhu
Ya kuma ce duk da ya yi wa jam’iyyar wakokin siyasa, amma kasancewarsa jekadan hukumar zabe mai zaman kanta INEC shi ya sa bai cika yin wakokin siyasa ba kada ya nuna ra’ayinsa.
“Wannan ra’ayi na ne ba zan yi wani abu ba har na fito da abin da ke rai na a fili.”
Jarumin ya kuma ce ba ya da uban gida a Kannywood, shi ne uban gidan kansa amma yana da abokan arziki.
Duk da amintaka da shakuwa da ake ganin tsakaninsa da Sani Danja, amma ya ce Ibrahim Mandawari ne ya fi burge sa a harakar fim.