Kannywood

Jaruma Maryam KK ta yi wa wani malami Raddi, wanda ya ce Almajiri daya da allonsa ya fi gaba daya Kannywood daraja

Jarumar Kannywood mai tasowa, Maryam KK ta nuna rashin jin dadinta akan kalaman zargin fasikanci da wani malami yayi wa ‘yan kannwood.

A cewarta, ba ya da wata kwakkwarar hujjar da zai kare kansa akan zargin da yayi musu a ranar tashin qiyama, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito..

Jarumar ta fara da wallafa bidiyon a shafinta sannan ta yi tsokaci karkashin bidiyon tana cewa:

Innalillahi wa inna ilayhi raji’un. Me ya hada almajiranci da Kannywood kuma? Babu wanda ya fi wani a wurin Allah sai wanda ya fi tsoronsa.

“Malam zaka iya shedar abinda ka fadi a ranar Lahira? Bara a musulunci haramun ne. Annabi SAW da kansa ya haramta yin bara.

“Wacce ake magana akanta bata zagi almajiranci ba. Kuma mun san darajar almajiranci. Shin a fin za ka ce babu nagari ko na banza?

“Da dana ya yi bara gara ya yi fim. Allah ka hana mu fadin abinda ranar lahira za a tashe mu bada shedar abinda muka fada ba mu da shi.

“Rayuwa kenan.

Tashar Tsakar Gida ta haska wa’azin wanda malamin mai suna Sheikh Kasim Abdullahi Damagum ya yi inda ya ke cewa Almajiri daya da alonsa ya fi Kannywood daraja a wurin Allah.

Ya ci gaba da cewa babu abinda ke cikin Kannywood fae iskanci da fasikanci. Ya ce almajiranci gaskiya ne don akwai gwanayen Qur’ani a cikinsu.

Ya ce duk wanda ya taba almajirai, su ya taba don haka ba za su kyale shi ba sai sun fito sun yi masa kaca-kaca ba tare da wani abu ya same su ba,labarunhausa na tattara bayanai

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button