Maganar Gaskiya Akan Shin Shugaban Jibwis Sheikh Abdullahi Bala Lau Ya Mutu Ko Yana Raye? – Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar IZALA a Najeriya JIBWIS na son sanar da al’umma cewa shugaban ta na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau na nan cikin ikon Allah a raye sabanin labarin karya da dandalin yanar gizo na “Sahara Reporters” ya yada cewa shehun malamin ya rasu kuma ba a ba da tazara tsakanin jama’a ba lokacin sallar jana’izar sa.
Sheikh Bala Lau wanda a yanzu haka ya ke Jimeta a jihar Adamawa na cigaba da gudanar da tafsiri ba tare da halartar jama’a ba; da a ke yadawa ta kafafen labaru don kalubalen korona bairos.
Don haka kungiyar Izala na bukatar dandalin sahara ya janye labarin karya da ya yada da rubuta ba da hakuri ga Imam Bala Lau da kuma kungiyar Izala da ke kan gaba wajen wayar da kan al’umma hanyoyin kula da lafiyar su daga wannan annoba da ta addabi duniya.
Kazalika kungiyar ta Izala na bukatar rubutaccen sako na ba da hakuri kan wannan labari na karya daga “sahara reporters”
Kin daukar wadannan matakan na ba da hakuri zai iya jawo matakin gurfanar da wannan kafa ta Sahara gaban kotu don diyyar wannan cin zarafi da yada karya a tsakanin al’umma.