google-site-verification=WmtThtgKMuimwQoXo8Cd4z9ZhII1jY-1XVfjGSvL5r8
Labarai

Ishara Allah Ya Yi Wa Gwamnatin Nijeriya Game Da Rikicin SARS, Wannan Somin Tabi Ne ~Sheikh Gumi.

 
Daga Indabawa Aliyu Imam
Fitaccen Malamin addinin musulunci a Nijeriya kuma kwararren likita Sheikh Dr Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa tashin-tashinar da ta faru ba komai ba ne illa ishara da Allah ke yi wa shugabannin Najeriya kan kusa-kuran da su ke aikatawa, kuma muddin ba su gyara ba wannan zai zama kadan daga abinda za su gani zuwa gaba.
“Ba zai yuwu ana kashe rayukan mutane ana salwantar da su ba, mutane na cikin tsananin yunwa da tsadar rayuwa ba, amma a danne bakin mutane a hana su yin korafi, sanda ‘yan Arewa su ka fara zanga-zangar Lumana kama shugannin zanga-zangar aka yi aka tsoratar da mutane”
Cewar shehin Malamin.
” Ko shekaranjiyar nan a Zamfara an kashe mutum ishirin da biyu, ban jima da dawowa daga Sokoto ba suna fad’a min mutum saba’in da tara aka kashe, kullum ne sai an yi wannan kashe-kashe, ga Fyade, ga dauke mutane, ga yunwa, ga talauci, ga cuta, ga rashin makarantu.
Duk da cewa an canza wannan zanga-zanga, sai dai babu wanda zai amfana daga hakan sai gwamnati, ba rushe SARS kawai ‘yan Najeriya ke bukata ba, akwai abubuwa da dama da jama’a ke bukata ayi wa garambawul, a fito kawai a fadawa gwamnati cewa ta na barci ana kashe mutane, kuma dole a tambaye ku jininsu gobe kiyama, mutane na mutuwa saboda yunwa, ana bin mutane ana sace su har gidajensu, kenan dole gwamnati ta tashi ta yi abinda ya kamata, kuma fadin hakan ga gwamnati shi ma Jihadi ne.
Manzon Allah S.A.W ya ce”
“ﻣﻦ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻛﻠﻤﺔ ﻋﺪﻝ ﻋﻨﺪ ﺳﻠﻄﺎﻥ ﺟﺎﺋﺮ .”
“Wato Jihadi mafi girma shi ne wanda mutum zai sami jarumta da mazantakar da zai fadawa shugaba gaskiya”
Duk gwamnatin da ba ta yarda a mata tsawa babu alkhairi a cikinta, domin ba wahayi ake mata ba dole a sami kuskure a cikinta, idan aka daki mutum ya yi kuka, kukan ya na nufin cewa mutumin nan zafi ya ke ji, amma mutane na mutuwa saboda yunwa saboda matakan gwamnati ta zartar.
Ba laifi ayi zanga-zanga don samar wa al’umma maslaha ko mafita, amma muddin zanga-zanga za ta bayu zuwa ga kashe-kashe ko salwantar dukiya hukuncinta haramun ne”, In ji Mufti Dr Gumi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button