Labarai

Budadiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Majalisar Wakilai Na Tarayyar Nigeria Akan Allurar Bill Gate ‘Microchip’ – Datti Asaalafy

Advertisment

  • Wannan wasika ce budaddiya zuwa ga Maigirma shugaban Majalisar Wakilai na tarayyar Nigeria Hon Femi Gbajabiamila da sauran ‘yan majalisarsa akan kudurin doka da yake so ya samar na tilasta wa dukkan ‘yan Nigeria karban allurar rigakafin cuta mai yaduwa wanda Bill Gate ya dauki nauyi.

Editan jaridar Thisday Mr Olusegun Adeniyi, Email: [email protected] ya wallafa bayani akan wannan batu tare da yin gamsasshen sharhi kwana uku da suka gabata wato ranar Alhamis 7-5-2020 da misalin karfe 12:04am na dare kenan, yace:
Maigirma shugaban majalisar wakilai na tarayyar Nigeria Hon Femi Gbajabiamila da wasu ‘yan majalisu guda biyu (Pascal Obi da Tanko Sununu) sun gabatar da kudurinsu na sabuwar doka a zama na daya da na zama na biyu akan batun dokar tilasta wa ‘yan Nigeria karban allurar rigakafin cuta mai yaduwa wanda Bill Gate ya dauki nauyi, amma sauran ‘yan majalisu da suka karbi kwafin takardan dokar hankalinsu ya tashi
Ba ni Datti Assalafiy na fada ba, Mr Olusegun Adeniyi ya fada cewa; Munji labarin mutumin da yafi kowa kudi a duniya Mr Bill Gate ya ware miliyoyin dalolin kudi ma wasu ‘yan majalisar zartawa a Nigeria domin su amince masa da dokar kakabawa ‘yan Nigeria karban allurar rigakafin cuta mai yaduwa, wanda a zahiri wannan allura na rigakafi zai cutar da mafi yawan ‘yan Nigeria tare da yin sanadin rage yawan jama’ar Nigeria.
Olusegun yaci gaba da cewa; bincike ya nuna ko a Kasar Amurka ne da zaran sun ji batun wani magani ko kiwon lafiya idan akwai hannun Bill Gate a ciki suna watsi dashi, a watan uku da ya gabata, akwai wani sanannen Malamin addinin kirista na Kasar Amurka mai suna Pastor Rick Wiles yayi gargadin cewa: “jini zai zuba a titunan Amurka idan aka kyale Bill Gate ya samu nasara yadawa mutane allurar rigakafinsa mai dauke da dalasiman shaidani abin bautarsa”
Ga bayanin da turanci: “There Will Be Blood in the Streets’ (of America) if Bill Gates continues to push for vaccinations in his bid to build ‘Lucifer’s Antichrist System”.
Pastor Rick Wiles yace; Bill Gate yana so ya sakawa mutane wani sinadarin microchip a jikinsu ta hanyar allurar rigakafi, yana son saka wannan abin a jikin ‘ya’yanku..
Ga bayanin da turanci: According to Wiles, “Bill Gates wants to get a microchip in your body, he wants a microchip in your baby’s body.”
Editan Jaridar Thisday Mr Olusegun Adeniyi yaci gaba da cewa; muna fuskantar wannan barazana da kalubalen na Bill Gate a Kasarmu Nigeria da ake so ayi amfani da Gbajabiamila wajen kafa dokar yin allurar rigakafi kamar yadda shugaban majalisar ya fada, wai yana son kafa wannan dokar ne domin a dakile shigowar cuta mai yaduwa a Nigeria ta hanyar allurar rigakafin da Bill Gate ya dauki nauyi. ~inji Editan jaridar Thisday Mr Olusegun Adeniyi
Na rubuta wannan wasikar ne a matsayina na Datti Assalafiy ‘dan Nigeria mai kare gwamnatin shugaba Buhari da jam’iyyar APC, a matsayina na Datti  Assalafiy mai bincike akan abubuwa da dama, hankalina ya tashi akan wannan kuduri na doka da Maigirma shugaban majalisar wakilai ke son ya tabbatar.
Maigirma shugaban Majalisar wakilai ya kamata ace ka fimu sanin manufar su Bill Gate jagororin “New World Order”, ka tuna da makomarka, da makomar ‘ya’yanka da makomar ‘yan Kasarka, don Allah kada ka goyi bayan jefa lamarin kula da kiwon lafiyarmu a hannun masu bautar shaidan, masu ganin cewa mutanen duniya sunyi yawa sai an rage ta kowace hanya
Kuma misali da abinda Pastor Rick Wiles yace; “Bill Gate yana so ya sakawa mutane wani sinadarin microchip a jikinsu ta hanyar allurar rigakafi, yana son saka wannan abin a jikin ‘ya’yanku”, bincike ya nuna da zaran an saka wadannan sinadarai a jikkunan mutane to nan gaba hankalin mutane zai juye, za’a sarrafa kwakwalwarsu yadda aka ga dama kamar yadda ake sarrafa na’ura mai kwakwalwa, don haka wannan mugun shiri na su Bill Gate na da matukar hatsari.
Kuma ko a dokar Nigeria ma tilasta mutane su karbi allurar rigakafi ba daidai bane, ya sa6a da kowace irin doka a Nigeria, yanzu ne dai ake so ayi dokar saboda manufar su Bill Gate, ku taimakemu kuyi watsi da kudurin su Bill Gate, don Allah ku dauki matakin dakike yaduwar cuta a Nigeria irin wanda Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) yayi bayani, yafi komai sauki
Yaa Allah Ka isar mana da wannan sakon zuwa ga inda ya dace, Allah Ka tausaya mana, Ka mana maganin abinda ya yafi karfin mu Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button