Labarai
Bidiyo: Yawan Duba Wayar Maza Na Jawo Rabuwar Aure ~ Laiylah Ali Othman ‘kawar Hadiza Gabon’
Advertisment
A tattaunawar da BBC ke yi da fitattun mutane a shafin Facebook da Instagram, mun tattauna da Laylah Ali Othman, wata ‘yar kasuwa a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin masu dumbin mabiya a shafukan sada zumunta a Najeriya.
A cewarta, me ya sa waya ke yawan kawo rabuwar aure? “Mene idan matarka ta ɗauki wayarka ta yi waya da ita ko ta ɗauki hoto.”
Laylah ta bai wa maza shawara kan cewa su goge duk wani abu da suke da shi a cikin wayoyinsu kafin su shiga gida.
Ta ce tun farko ma babu amfanin mata su rinƙa duba wayoyin mazajensu, domin kuwa idan mata za su riƙa duba wayoyin mazanjensu, to akwai yiwuwar za su fuskanci ɓacin rai ko kuma ma a rabu gaba ɗaya.
Amma a cewarta, idan ta auri mutum, dole ta san duka sirrin da ke cikin wayarsa.
A tattaunawar da aka yi da Laylah, ta bayyana cewa ta yi aure har sau biyu, amma ba ta ji daɗin zaman auren ba.
Ta ce tana da burin yin aure a nan gaba, ta ce ta yi auren har sau biyu ba amma ba ta ji daɗinsa ba.
A cewarta, a halin yanzu tana da masoyi wanda ta ke sa ran aura, kuma nan gaba kaɗan za ta ba mutane mamaki.
Cikin wadanda suka turo saƙonni yayin tattaunawar, an tambayi Laylah kan cewa bayan gidan abinci da kuma kayan ɗaki da take sayarwa nan gaba kuma me za ta ƙara fitowa da shi?
A amsar da ta bayar, cewa ta yi “asibti, ina gina asibiti a Yobe yanzu haka Insha Allah, ina so na kai musu asibitin da za su samu duk wata kula da suke buƙata yadda ba sai sun je asibitin koyarwa na Maiduguri ba”.
‘Ba a fahimce ni ba kan batun maza’
Ta bayyana cewa mutane da dama na mata mummunar fahimta dangane da yadda take bayani kan maza, ta ce ba wai tana cewa ba ne duka maza ba su da kirki.
A cewarta, akwai na kirki, ta kuma lissafo mahaifinta da wasu surukanta da kuma wasu maza da dama da ta ce ta sansu kuma suna da kirki.
Jama’a da dama masu bin Laylah Othman a shafin Instagram na yawan zarginta da wallafa duk wani aikin alkhairi ko kuma na taimako da take yi. Sai dai a cewarta, tana da dalilin yin hakan, ta ce tana yin haka ne domin jawo ra’ayin wasu don su yi aikin alkhairi irin nata.
Ta ce kashi 90 cikin 100 na ayyukan alkhairin da take yi ba ta nunawa, ”kaɗan ne daga ciki ne nake nunawa kuma ba zan daina nunawa ba, in ji Laylah.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment