CORONAVIRUS : Karanta Irin Kokarin Taimako Da Jaruma Maryam Booth Ta Dauka Kan Cutar Covid 19
Maryam Booth Tayi Alkawarin Bada Tallafin Buhun Siinkafa 100, Da Kwalin Ajinomoto 100, Da Jarkar Mai 50 Ga Marasa Karfi
Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Jarumar Kannywood Maryam Booth tayi alkawarin tallafawa marasa karfi a wannan lokaci da cutar Coronavirus, tasa wasu jihohin suka bada sanarwar zama a gida.
Jarumar ta bayyana yunkurin bada tallafin ne a shafinta na Twitter jarumar tayi hakanne don ragewa marasa karfin radadin wannan lokaci.
Inda tace zan bayar da buhun shinkafa guda dari (100), da kwalin magi ajinomoto guda dari (100), da kuma jarkar mai guda hamsin (50), ga marasa karfi.
Tace idan kun san wani wurin ‘yan gudun hijira ku sanar dani dan Allah ta hanyar sanya adireshi a bangaren sharhi, tace mutane na za su kai musu dauki.
Jarumar dai itace ta farko cikin jaruman Kannywood data fito ta bayyana kudirinta na tallafin abinci a dai dai wannan lokaci.
A dai lokacin da jarumar ta sanar da wannan kudiri nata wasu da suka bayyana raayinsu sun yaba mata inda sukai mata fatan alkairi.
Sai dai wasu sunyi korafi inda suke ganin kamata yai ta bayyana tallafin nata ga kowa ba iya yan gudun hijra ba kamar yadda ta fada.
Yayi kyau Allah ya bada lada.
Daga wayesuloaded.com.ng boss.
Ameen.