Kannywood
Shin Da Gaske Mahaifin Nura M Inuwa Ya Rasu ? – Nura M Inuwa
A yan kwana kin nan ana yayatawa da cewa mahaifin shahararren mawakin nanaye nura m inuwa yayi jawabi a shafin na facebook.
Ga jawabin mawakin
“Mahaifina Ya na Raye cikin koshin Lafiya.
An janyo hankalina bisa wani rubutun ‘Karya da aka wallafa a shafin Facebook da ke bayyana Rasuwar Mahaifina.
Wannan zance kirkirarre ne, Babu kamshin gaskiya, Mahaifina ya na nan a Raye cikin koshin Lafiya.
Ina Kira ga masoyana su kwantar da hankalinsu , Su Yi watsi da wannan maganar, Kuma duk Wanda yayi Karo da rubutun a Facebook yayi report dinsa ga hukumomin Facebook domin su cire rubutun.
– Nura M. Inuwa
13 – Oct – 2020″