Zan Bi Diddigin Kisan Matashi Mus’ab Har Sai Gaskiya Ta Yi Halinta, Cewar Sheikh Pantami
Daga Bala Aminu
Ministan harkokin sadarwa na ƙasa Sheikh Dakta Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai bi bahasin yadda wani ɗan sanda ya hallaka matashin mai suna Mus’ab Sammani a birnin Kano sakamakon wata ƴar taƙaddama da ta faru tsakanin matashin da wani mai tuƙa babur ɗin adaidaita sahu.
Sheikh Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, in da ya sha alwashin zai bi kadin binciken yadda lamarin ya faru har sai gaskiya ta yi halinta.
“A ƙashin kai na ni Isa Ali Pantami zan bi bahasin wannan al’amari har sai na ga an tabbatar da gaskiya In Sha Allah. Shi kuma marigayin Allah ya yi masa rahama amin”
Idan za’a iya tunawa dai a ranar Talata ne wani jami’in ɗan sanda da ya ke aikin gadi a bankin Union ya harbe Mus’ab har lahira sakamakon wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsa da wani direban babur ɗin adaidata sahu.
Tuni dai kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.