Labarai

Gwamnatin Taraiya ta dawo da tallafin mai – Shugaban kamfanin Rainoil

Shugaban Kamfanin mai na Rainoil, Gabriel Ogbechie, ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta dawo biyan tallafin man fetur sakamakon karya darajar Naira a kasuwar canjin kuɗaɗe.

Daily Trust ta rawaito cewa Ogbechie ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin wata liyafa da bankin Stanbic IBTC ya gudanar a Legas.

Ya yi nuni da cewa, yadda ake amfani da man fetur a Najeriya a kullum a kan lita miliyan 40, sannan kuma farashin kudin kasashen waje a kan Naira 1,300, tallafin da gwamnati ke biya a kan kowace litar man fetur ya kai tsakanin Naira 400 zuwa 500, wanda ya kai kusan Naira biliyan 600 a kowane wata.

Yace; “Lokacin da shugaban kasa ya zo a watan Mayun bara, daya daga cikin abubuwan da ya ce shi ne tallafin mai ya tafi. Kuma da gaske, tallafin ya tafi, domin nan da nan farashin man fetur ya tashi daga 200 zuwa 500 kowace lita. A lokacin da gaske, tallafin ya tafi.

“A wancan lokacin ana musayar Dala kan Naira 460, amma bayan ‘yan makonni sai gwamnati ta karya darajar kudin. Kuma Dalar ta koma kusan N750. To tun a wannan lokacin, tallafin ya fara dawowa.

“Lokacin da aka rufe kasuwannin biyu a hukumance, a hukumance kasuwar ta kai kusan N1,300. A wannan lokacin, maganar ta baiyana. Tallafin mai ya dawo. Idan kana son sanin yaya man fetur ya ke duba kawai inda dizal yake. Diesel dai ya kai kusan N1,300 kuma har yanzu ana siyar da man fetur akan N600.

“Bugu da kari, ya ce kamfanin mai na kasa NNPC kasancewar shi kadai ne mai shigo da mai a kasar nan yana nuni da cewa ana ci gaba da bayar da tallafin, domin sai an gyara farashin,” in ji shi.

Ko a jiya ma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i, ya ce gwamnatin tarayya na biyan kudaden tallafin man fetur fiye da na da ma.

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button