Labarai
Magoya Bayan Kwakwasiyya Da Gandujiyya Sun Gwabza A Hawan Daushe
Rahotanni daga birnin Kano sun nuna cewa an ji wa mutane da dama rauni ciki har da wasu manyan jami’an tsagin siyasar Kwankwasiyya bayan da ‘yan daba suka farma mutane a wurin hawan Daushe.
A bisa rahotanni wasu ‘yan adaban, wadanda ake zargin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, sun farma magoya bayan Tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso, wadanda suka yi fitar dango da jajayen hulanansu. Suka kara da cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa an yanke su ne da wuka yayin da aka sari wasu da manyan makamai, kamar adda da takofi. Hawan daushe, wanda sarkin Kano ke jagora kwana daya bayan kowacce sallah, na jan hankalin jama’a da dama ciki har da ‘yan yawon bude ido.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com